✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Zanga-zangar EndSARS ta jawo asarar biliyan N400 a Legas

Gwamnatin Jihar Legas ta yi asarar kusan Dalar Amurka biliyan daya sakamakon tarzomar da ta barke a jihar a dalilin zanga-zangar #EndSARS. Shugaban Cibiyar Kasuwanci…

Gwamnatin Jihar Legas ta yi asarar kusan Dalar Amurka biliyan daya sakamakon tarzomar da ta barke a jihar a dalilin zanga-zangar #EndSARS.

Shugaban Cibiyar Kasuwanci a Legas, Muda Yusuf, ya bayyana cewa ba a gama tattara hakikanin alkaluman asarar da tarzomar EndSARS ta jawo ba, amma kawo yanzu asarar da aka gano ta haura Dala biliyan daya, kwatankwacin Naira biliyan 400.

Ya ci gaba da bayyana cewa “An shafe akalla sati biyu da fara lalata tattalin arzikin Legas da na Najeriya sakamakon zanga-zangar, ganin cewa Legas ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya,” kamar yadda ya fada.

A cewarsa, idan aka samu tsaikon tattalin arziki a Legas, tasirin da zai yi ga Najeriya yana da yawa, kuma zai dauki lokaci mai tsawo kafin ya murmure.

“Gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari sun tabka asara.

“An yi asarar sama da kadarori 100 kuma ba wai kanana ba”, a cewarsa.

Kadarorin da aka rasa sun hada da ofisoshi da kamfanoni da masana’antu da dama.