✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EndSARS: Yadda bata-gari ke sheke ayarsu a Legas

Sama da sa'a 24 'yan daba da sauran bata-gari na cin karensu babu babbaka a Jihar Legas

Barayi da ’yan daba na cin karensu babu babbaka suna fasa shaguna da cibiyoyin kasuwanci suna kwashe kayan jama’a a jihar Legas.

Yayin da mazauna suka rufe harkokinsu bayan dokar kulle da gwamnatin jihar ta sanya, ’yan daba dauke da muggan makamai na amfani da damar suna tafka ta’asa.

Satar dukiyoyi da tsaka rana

A ranar Laraba, daruruwan ’yan daba sun fasa babban shagon kasuwanci na Shoprite a unguwar Lekki suka debe kaya babu mai ce musu kanzil.

Sun kuma farfasa shagunan da ke makwabtaka da wani banki a unguwar suna kwasar kaya.

Halin da jihar Legas ta tsinci kanta ya faru ne bayan zanga-zangar EndSARS ta kazance tare da sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Fakewa da EndSARS domin ta’adi

Matasan da suka fake da zanga-zangar sun kai hari a gidan Oba (Sarki) na Legas, inda suka lalata kadarori tare da sace abin da za su iya.

Daga bisani an gan su rik da sandar girman sarkin a kan titi suna yawo bayan sun yi ta kwasar kaya daga fadarsa.

Wani bidiyon da ke yawo a intanet ya nuna yadda matasa ke ta kwasar kaya daga ginin wani Babbar Kotun da ke unguwar Igbosere.

A ranar Talata matasa suka sa wawa a kan kayan Sakatariyar Karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun da ke jihar suka kuma banka wa ginin wuta.

Kazancewar zanga-zangar EndSARS

A ranar ce aka sanya dokar hana fita a jihar bayan zanga-zangar ta EndSARS ta kara kazancewa har ta kai ka kashe mutum uku da safe a wata arangama tsakanin ’yan kungiyar asiri da wasu ’yan tireda.

Bata-garin da suka shige cikin zanga-zangar sun kashe jami’an tsaro tare da kona gine-ginen gwamnati da kadarorin ’yan kasuwa tun daga ranar Talata.

Bayan sanya dokar hana fita da gwamnatin jihar ta yi, wasu matsa sun banka wa wasu tireloli dauke da shanu wuta a abbatuwa.

Bijire wa doka dokar hana fita

Masu zanga-zangar sun yi fatali da dokar hana fitar da jihar ta sanya da za ta fara aiki a karfe hudu na ranar.

Sun yi ta gudanar da taronsu har bayan magariba, lamarin da ya kai ga sojoji suka je inda suka taru a unguwar Lekki domin tarwatsa su.

Daga bisani gwamnan jihar ya kara lokacin farawar dokar zuwa karfe na dare sannan ya bukaci jami’an tsaro da kar su tsare wadanda suka karya dokar.

Mazu zanga-zangar sun yi zargin harbin da sojojin suka yi a wurin ya hallaka mutum 27 daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama.

Sai dai a safiyar Laraba bayan zagayen dubiya a asibitocin da aka kwantar da wadanda abin ya shafa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, a jawabinsa ya ce ba a samu asarar rai ba, amma an raunata mutum 27.

Jawabin nasa ya haifar da karin ce-ce-kuce bayan caccakar da aka yi wa sojoji na bude wa masu zanga-zangar wuta.

Kone-kone fusatattun ’yan EndSARS

Da safiyar Laraba fusatattun masu zanga-zanga sun banka wa muhimman wurare wuta da suka hada da Hedikwatar Hukumar Jiragen Ruwa (NPA).

Sun kuma kona tashar motocin gwamnatin jihar ta BRT tare da dukan duk wanda suka yi karo da shi.

SUn koma kai hari a ofishin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da na hukumar kula da lafiyar ababen hawan (VIO), suka banka musu wuta, duk a unguwar Lekki.

Gidan talabijin na TVC, mallakin jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Bola Tinubu na daga cikin wuraren da aka kona.

Kazalika an kona gidan mahaifan gwamnan jihar da wasu wurare.