✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Enugu Rangers ta yi tankade da rairaya

A ranar Litinin da ta gabata ce mahukunta kulob din kwallon kafa na Enugu Rangers suka yi tankade da rairaya ga daukacin ’yan kwallon da…

A ranar Litinin da ta gabata ce mahukunta kulob din kwallon kafa na Enugu Rangers suka yi tankade da rairaya ga daukacin ’yan kwallon da ke yi wa kulob din wasa.

Janar Manajan Kulob din, Mista Dabid Owunmi ne ya sanar da daukar wannan mataki ga manema labarai a Enugu.

Daga cikin matakan da kulob din ya dauka akwai mayar da ’yan kwallo 8 da ke buga wa babbar kungiyar zuwa karamar kungiyar sannan an zaftare wa daukacin ’yan wasan gaba na kulob din albashi da kashi 40 inda za su rika karbar kashi 60 kacal daga cikin 100 har lokacin da abubuwa za su gyaru.

Janar Manajan ya ce wannan mataki da suka dauka yana bisa doka, don tun kafin su kulla yarjejeniya da kowane dan wasa sai da ya sanya hannu game da daukar irin wannan mataki.  Ya ce sun yi haka ne don su karfafa wa ’yan wasan gwiwa wajen zage damtse su fitar da kulob din daga halin da yake ciki a bana.

Kawo yanzu kulob din Enugu Rangers yana  kusa da karshe ne a jerin kungiyoyi 20 da ke fafatawa a gasar Firimiya ta Najeriya.