Da Dumi Dumi

Enyimba ta kori mai horas mata da ’yan wasa

Usman Abdallah

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Enyimba dake garin Aba Jihar Abiya ta sallami mai horas da kungiyar Usman Abdalla. Shugaban kungiyar Felid Anyasi -Agwu ne ya bayyana sanar da korar ranar litinin din nan da ta gabata cikin wata sanarwa da aka raba wa manema ciki har da wakilin Aminiya.

Felid Anyansi-Agwu, Ya ce ya zame wa kungiyar dole ta dauki wannan matakin gaggawa na korasa  sakamakon zargin rashin tabuka wani abin a zo a gani tun daga lokacin da kakar wasa ta bana ta fara “mun lura maimakon kungiyar ta ci gaba ta rika samun nasara a wasanninta sai ma akasin haka ake rika samu.”

Hukumar gudanarwar kungiyar ta nada  Fatai Osho ya ci gaba da jan ragamar kungiyar.  Anyasi-Agwu ya kara da cewa hukumar kungiyar kwallon kafar ba ta yi garaje ba wajen sallamar mai horas da kungiyar sai da ta bi mataki a hankali ta yanke shawarar hakan in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “Tun daga lakacin da kakar wasa ta fara mun lura babu wani abin kirki da ya kulla wa don haka kungiyar babu wani ci gaba ta ta samu.”

Da ya juya kan ’yan wasan kungiyar,  shugaban na Enyimba ya gargade su da su kara kwazo fiye da wanda suke da shi a yanzu wajen wasa in ba haka  ba kuwa duk za su san inda dare zai masu . Kungiyar ta yi wa Usman Abdallah fatar alheri  a duk inda ya koma.

ADVERTISEMENT

A waje daya kuma ana zargin cewa hukumar gudanarwa ta kungiyar ce tare da kungiyar masu goyon bayan Enyimba suka tilasta wa Koci Usman Abdallah ya yi murabus biyo bayan kashin da kungiyar ta sha a gida ranar Lahadin da ta gabata da ci 4-0 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Plateau United. Don haka jin cewa hukumar gudanarwar kungiyar ta sha alwashin korarsa a washe garin ranar Litinin sai ya riga su ya rubuta takardar ajiye aikinsa.

Enyimba dai ba ta samu nasara ba a wasanni biyar na baya-bayan nan da ta buga ciki har da na wanda take bugawa na gasar nahiyar Afirika.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya