✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Enyimba ta sayo ’yan kwallo 3 ’yan Ghana

Kulob din Enyimba da ke Aba ya bayar da sanarwar sayo wadansu ’yan kwallo uku ’yan Ghana da biyu daga cikinsu ke wasa a kulob…

Kulob din Enyimba da ke Aba ya bayar da sanarwar sayo wadansu ’yan kwallo uku ’yan Ghana da biyu daga cikinsu ke wasa a kulob din Asante Kotoko da ke Ghana yayin da dayan ke wasa a kulob din Delta Force a Najeriya.

Kamar yadda kulob din ya sanar a shafin sadarwasa na Twitter a ranar Talatar da ta wuce, ya ce ya sayi ’yan kwallo ne  a kokarin tunkarar kaka ta bana da kuma fuskantar  gasar cin Kofin Zakarun Afirka (CAF Champions League) da za a fara a wannan mako.

’Yan kwallon da kulob din ya sayo daga kulob din Asante Kototo sun hada da Daniel Darkwah da kuma Abbas Mohammed. Daya dan wasan shi ne Emmanuel Ampiah dan asalin Ghana da ke wa kulob din Delta Force a Najeriya kwallo.

Kulob din Enyimba ne ya lashe gasar rukuni-rukuni ta Najeriya a bana, inda hakan ya sa zai wakilci kasar nan a gasar cin Kofin Zakarun Kulob-Kulob na Nahiyar Afirka da za a fara a wannan mako.