✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Eto’o zai kawo ziyara Najeriya

Tsohon dan kwallon Najeriya kuma  Jakadan Gasar La-Liga ta Spain a Najeriya Mutiu Adepoju ya ce Samuel Eto’o tsohon dan kwallon Kamaru da kulob din…

Tsohon dan kwallon Najeriya kuma  Jakadan Gasar La-Liga ta Spain a Najeriya Mutiu Adepoju ya ce Samuel Eto’o tsohon dan kwallon Kamaru da kulob din Barcelona na Spain zai kawo ziyara Najeriya nan da karshen watan da muke ciki.

Adepoju ya ce Eto’o zai ziyarci kasar nan ce don ya kalli wasan El-Clasico a tsakanin kulob din Real Madrid da na FC Barcelona a akwatin talabijin tare da masoyansa da ke kasar nan.

Sai dai Adepoju bai bayyana gari ko jihar da Eto’o zai kalli wasan tare da masoyansa a kasar nan ba.

Adepoju wanda ya taba yin  kwallo a Spain ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar The Punch ta ranar Lahadin da ta wuce.

Ya ce a matsayinsa na Jakadan Gasar La-Liga ta Spain ya kulla yarjejeniya da Samuel Eto’o don ya ziyarci Najeriya a karshen wannan wata don ya kalli fafatawar da za a yi a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Spain wato Real Madrid da FC Barcelona a wasan El-clasico a ranar Lahadi 1 ga Maris.

Adepoju ya kara da cewa baya ga Eto’o, kungiyarsa na yunkuyrin gayyato Lionel Messi nan gaba don shi ma ya kawo ziyara Najeriya don ya gana da masoyansa.

“Muna shirin gayyatar manyan ’yan kwallo a sassan duniya ciki har da Lionel Messi don su kawo ziyara Najeriya saboda su hadu da masoyansu,” inji Adepoju.

Adepoju mai shekara 49 ya kwashe kimanin shekara 7 yana wasa a Spain inda ya zura kwallaye 22 a raga. Bayan ya bar kwallo ne sai ya zama Jakadan Gasar La-Liga ta Spain inda yake kulla zumunci a tsakanin mahukunta gasar da Najeriya.