Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Fadakarwa: Yau saura kwana 43 zabe

Fadakarwa: Yau saura kwana 43 zabe

Yau 4 ga Janairu 2019, a kidaya saura kwana 43 a yi zaben Shugaban Kasa, idan Allah Ya kai mu Asabar 16 ga Fabrairu, 2019. A yau GIZAGO (08065576011) zai ci gaba da tsokacinsa ne don fadakar da al’ummar kasa dangane da zaben mai zuwa:

A yau maudu’inmu zai duba batutuwa da dama da suka danganci al’amuran rayuwarmu, misali kamar cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar al’umma, domin kuwa ko a kwanakin baya a yayin muhawara tsakanin ’yan takarar Mataimakan Shugaban Kasa, al’amarin da Mataimakin Shugaba Buhari, Yomi Osinbajo ya tabo ke nan. Ya nuna yadda gwamnatin PDP ta kassara kasar nan a tsawon mulkinta na shekara 16, yadda komai ya lalace saboda almundahana da dukiyar al’umma da suka yi.

ADVERTISEMENT

A yayin da Peter Obi na PDP ya ce bai kamata Gwamnatin Buhari ta buge ga yaki da barayi ba, shi kuwa Osinbajo cewa ya yi, idan ka bar shagonka ga barayi, za a wayi gari sun sace komai. Don haka dole ne mu mai da hankali wajen tattalin dukiyar al’umma da yin aiki da ita yadda ya dace, domin gina kasa don amfanin ’yan kasa.

A wannan janibi, ya kamata al’umma su nuna goyon baya ga Osinbajo, cewa lallai ne mu zabi shugaban da zai kare tattalin arzikinmu daga almundahana da babakere. Lallai ne mu yaki cin hanci da rashawa da almundahana. Ke nan, ya kamata a wannan zabe mai zuwa, mu bibiyi kudirorin ’yan takararmu duka. Mu zabi wanda ke da kudirin yaki da almundahana ka’in-da-na’in kuma da gaske. Mu kiyayi wanda zai mai da mu gidan jiya, wanda zai bude kofa ga barayin dukiyar al’umma. Mu kiyayi wanda zai mai da dukiyar al’umma ganima domin rarraba ga ’yan uwa da abokan arziki da iyalai.

ADVERTISEMENT

Idan ana batun almundahana da kashe-mu-raba da cin hanci da rashawa, mafi yawan lokaci akan saka jami’an tsaro cikin da’irar tunani.

Idan an ce jami’an tsaro, ana nufin dukan wadansu barade ko jami’ai da hukuma ta dora wa alhakin kula da harkokin tsaron al’ummar kasa. Wadannan kuwa sun hada da ’yan sanda, soja, sibildifens, kwastam, magireshin da sauransu. Kuma babu shakka suna da gagarumar rawar takawa a yayin zabubbukan da ke tafe a Fabrairu mai zuwa. Don haka, abu ne mai kyau da kishin kasa, jami’an tsaro su kaurace wa almundahana da amsar rashawa yayin aikinsu.

Ya ku jami’an tsaro! Ku sani cewa kundin tsarin mulkin kasa ya raba muku aiki daidai da ku, kuma kun yi rantsuwar kama aikin kare lafiya da dukiyar al’ummar kasa. Don haka ya kamata ku sani cewa amana ce kuka dauka a kanku, don haka ku yi kokari ku gudanar da aikinku bisa gaskiya da amana. Ku kiyayi cin hanci da rashawa, ku sani cewa cin rana daya kumburin ciki ne. Kuma ha’incin da za ku yin a lokaci daya, zai iya jefa kasar nan da al’umarta cikin ukubar dindindin, wanda haka zai shafe ku da sauran al’ummar kasa, ciki har da ’ya’yanku da jikokinku, wadanda ba su zo duniya ba yanzu.

Ya al’ummar Najeriya! A matsayinmu na ’yan kasa, ya dace mu gane muhimmanci da tasirin kishin kasa da kuma dangantakar da ke tsakanin kasar tamu da mu kanmu.

Abu na farko da ya kamata kowane dan kasa ya gane shi ne, kasarka ita ce alkiblar rayuwarka. Abin nufi shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin kasar nan kake. Ya alla kana kauye ne ko birni, kai dan kasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a karkashin karamar hukuma, a karkashin jiharku; wadanda su kuma suke a cikin Najeriya.

Kasancewar ba ka da wata kasa da ta kai kasarku, lallai ne ka mai da hankali wajen nuna kishinta da kare martabarta, domin  idan ta kasance mai muhibba da martaba, to kai ne ka zama mai martaba da muhibba. Idan ta zama ballagaza, marar kima a idanun duniya, to ka sani kai ma haka kake.

Domin ganin ka zama mutum nagari, mai kima da martaba, sai ka tashi tsaye, ka yi kokari iya yin ka, wajen bunkasa kasarka. Dalili na farko ke nan da ya sanya za ka zama mai kishin kasa.

Bari in kara wata tambayar, shin ta yaya za ka zama mai kishin kasa? Ta yaya kishin kasarka zai amfane ka, ya amfani al’ummar kasarka da ita kanta kasar?

Yana daga cikin kishin kasa, ka kasance mai gaskiya da amana a cikin al’amuranka. Idan ka kasance mai fadar gaskiya kuma kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan ka kasance mai rikon amana wajen mu’amalarka da mutane, to kuwa kasarka za ta zama mai gaskiya da amana, abar kauna ga al’ummar duniya. Dalili shi ne, a matsayinka na dan kasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da amana. Idan ka zama haka, wancan ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; shi ke nan an samu abin da ake so. Kasarmu za ta cika da masu gaskiya da amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintacciya mai aminci a cikin kawayenta na sassan duniya.

Kishin kasa ne ga dan kasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wanda ba ya aiki ko sana’ar komai. Da zarar dan kasa ya zauna dirshan ba tare da yana wata harka ba, babu wanda zai zame masa aboki sai Shaidan. Wannan zaman banza zai bijiro masa da tunane-tunane marasa kyau, sannan su ingiza shi zuwa aikata munanan ayyuka, wadanda za su kasance hallaka a gare shi kuma su cutar da sauran al’umma. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi kasarsa, domin kuwa sunanta zai baci ta hanyar munanan ayyukansa.

Don haka, ya dace mutum ya mike tsaye ya sama wa kansa abin yi. Kada mutum ya ce zai zauna sai ya samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Koda ka gama jami’a ne, idan ba ka samu aiki ba, yi kokari ka fara koda aikin karfi ne na kwadago. Dan abin da za ka samu, zai iya zama mai albarka kuma ka biya bukatarka da shi. Kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunkuri da ka yi na aikin karfi, Allah na iya hada ka da wata sila, wacce za ka iya samun aikin da ya fi shi.

Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci koda da karamin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya ko ruwan leda. Sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka rika samu, matukar kana adanawa da kadan-kadan; jarinka yana iya zama mai girma. Idan har ka rika gudanar da harkarka cikin gaskiya da tsare hakkin jama’a, kasuwancin naka yana iya zama mai albarka. Domin akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da kankanen jari kuma suka bunkasa har suka zama hamshakan ’yan kasuwa.