Da Dumi Dumi

Fadakarwa: Yau Saura Kwana 50 Zabe

Yau Jumu’a, 28 ga Disamba 2018, saura kwana 50 daidai a yi zaben Shugaban Kasa idan Allah Ya kai mu Asabar 16 ga Fabrairu, 2019. A yau GIZAGO (08065576011) tsokacinsa ya fadakar da al’ummar kasa ne dangane da zaben mai zuwa:

Ka sani, kai dan siyasa, ba za ka iya jagorancin kasar nan cikin nasara ba har sai al’umma sun samu hadin kai, sun samu fahimtar yadda za su yi amfani da bambance-bambancensu wajen bunkasa kasa da baiwar da Allah Ya ba kowa. Domin kuwa tunda Allah Ya kadarta zamanmu a kasa daya, muna bukatar juna muddin muna son ci gaban al’ummarmu da kasarmu baki.

Ya kai dan siyasa! Ka sani Hausawa suna cewa gani ga wane ya isa wane tsoron Allah, kamar yadda suka ce, abokin damo guza. Me nake nufi da wadannan batutuwa? Ina nufin ya kamata ka dauki izna da dauki misali da wasu kasashe da wadansu ’yan siyasa na wasu kasashe. A lokacin da ka samu kanka bisa kujerar mulki, ka yi abota da kasar da za ta karfafi kasarka ta fannonin kirki. Kada ka yi kawance da kasa ko Shugaban Kasar da zai cuci al’ummarka.

Ka sani cewa shugaban da ke kishin al’ummarsa shi ne ke fita waje ya jawo wa kasarsa arziki, ba wai ya gayyato mata tawagar ’yan ta’adda ba. Ka zama mai kudirin alheri ga al’umma.

Ya kai dan siyasa! Ya kamata ka bambanta da wasu kurayen shugabanni da ke kwashe dukiyar talakawa su kai kasashen waje su kimshe. Wannan kashe kasa ne, kashe al’umma ne. Ka sani, dabba ma fita take daga gidanta, ta samo albarka ta kawo gida, ba wai ta dauki na gidanta ta kai waje ba.

ADVERTISEMENT

Ya kai mai son mutane su zabe ka a matsayin SHUGABA, ka zama mai KISHIN KASA!

Ya kai dan siyasa mai hankoron tara dukiya! Ya kamata ka san cewa, shi mulki hidima ne ga al’umma. Idan ka yi wa al’umma hidima, ita ce mizanin da za a auna kimarka a tarihinka ko bayan babu kai. Ka sani cewa idan ka tara dukiya, kai kadai da iyalanka za ta amfana, idan ma ta amfana ke nan. Idan kuwa ka yi amfani da dukiyar kasa ka yi wa al’umma aiki, ka amfani kanka, ka amfani al’ummar kasa kuma ko bayan babu kai, za a yi ta yi maka addu’a.

Akwai misalin shugabanni abin koyi a nan gida Najeriya da wasu kasashen Afirka da suka shuka alheri kuma har yau ake tunawa da su. Dauki misalin marigayi Nelson Mandela na Afirka ta Kudu da Julius Nyerere na Tanzaniya da sauransu. A nan gida Najeriya ma, akwai irin su marigayi Abubakar Tafawa Balewa da Sardauna Ahmadu Bello da Janar Murtala Muhammad.

Wadannan shugabanni, ba su tara dukiya ba, amma sun tara ayyukan alheri da a kullum ake tunawa da su. Don haka, ya kai DAN SIYASA! Ka yi koyi da su, domin kai ma al’umma ta yi alfahari da kai.

Ke ma Hukumar Zabe da jami’anki, kamar yadda tsarin mulki ne ya samar da ke, sannan ya shirya miki tsare-tsare da dokoki, haka kuma ya tanadar da jami’an da za su gudanar da wannan zabe akwai bukatar ku kara daidaita sahu. Don haka tun daga Shugaban Hukumar, har zuwa ma’aikaci mai matsayi mafi karanta a hukumar, kuna da aiki mai girma a gabanku.

Ku sani cewa wannan aiki amana ce a kanku, don haka matukar kuna son kasancewa ciki-lafiya-baka-lafiya, to ku sanya gaskiya da tsoron Allah a yayin gudanar da shi. Kullum, kasar nan da al’ummarta za ku sanya a zukatanku. Ku kasance kun gudanar da aikinku bisa kwarewa da sanin ya kamata, ba nuna son kai ko bangaranci ba.

A kwanakin baya ma an jiwo Shugaba Muhammadu Buhari yana cewa: “Ina kira ga Hukumar Zabe Ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) da dukan hukumomin tsaro na kasa su sanya kasar nan a zukatansu a yayin gudanar da ayyukansu. Duk duniya tana kallonmu kuma gagarumin aikin gina kasarmu da sanya aminci a cikin tsarin siyasarmu da tafiyar da ita shi ne kashin bayan ci gaba da bunkasar kasarmu.”

Wannan bayani na Shugaban K’asa, ma’anarsa a bayyane take kuma aiki da shi zai zama mai matukar muhimmanci ga kanmu da al’ummarmu da kasarmu baki daya.

Shi ma Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a kwanakin baya ya ja hankalin ’yan siyasa dangane da yadda wadansunsu suke ingiza matasa wajen bangar siyasa. Ya gargadi ’yan siyasa su daina daukar ’ya’yan wadansu suna lalata musu rayuwa, suna saka su cikin bangar siyasa.

Sultan ya yi wannan gargadi ne a Sakkwato a kwanakin baya, wajen taron wayar da kan al’umma dangane da zabe mai zuwa, wanda Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Kasa (NOA) ta shirya.

Chiroman Sakkwato, Alhaji Buhari Abubakar ne ya wakilci Sarkin Musulmin, inda ya shaida wa ’yan siyasa cewa su tuna cewa Allah ne ke ba da mulki ga wanda Ya so, don haka su rika gudanar da siyasa cikin tsabta, ba wai wani abin ko-a-mutu-ko-a-yi-rai ba.

Shi kuwa Daraktan Hukumar NOA na Jihar Sakkwato, Maude Danchadi, gargadi ya yi ga ’yan siyasar kan su guji mummunar dabi’ar nan ta sayen kuri’a daga mutane kuma su kiyayi kiyayya da gaba a siyasa.

Don haka a wannan gaba zan karkata ne zuwa ga ita kanta Hukumar NOA. Wannan hukuma tana da babban aiki mai matukar muhimmanci, na fadakar da al’umma kan abin da ya shafi kakar zabe mai karatowa. Don haka ya kamata ta tashi tsaye ta tunkari aikin wayar da kan al’umma da gaske, domin kuwa masu iya magana suna cewa, bori ba ya son sanyin jiki.

Lallai ne wannan hukuma ta NOA ta yi hadin gwiwa da malaman addinai da ’yan jarida da sauran masu aikin fadakarwa domin taya su wannan aiki. Ana bukatar a fadakar da su kansu ’yan siyasa da matasa maza da mata, domin su kasance masu gudanar da al’amura bisa dacewa da dokar kasa dangane da wannan zabe mai zuwa.

 

NOA ki tashi tsaye ki kama aiki, domin kuwa lokaci ya yi!

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya