Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Fadan Kabilanci: Sojoji sun kama mutum 71a Adamawa

Gwamnan Jihar Adamawa Muhammadu Bindow Jibrilla
Gwamnan Jihar Adamawa Muhammadu Bindow Jibrilla

Kwamandan Birged din Sojoji na 23, Birgediya Janar Bello Muhammed ya mika mutum 71 da sojoji suka kama kan zargin haddasa fadace-fadacen kabilanci a tsakanin kabilar Waja da Luguda a kananan hukumomin Lamurde da Guyuk na Jihar Adamawa ga ’yan sandan jihar domin gudanar da bincike a kansu.

Janar Muhammad ya ce sun kama mutanen ne bayan sun dauki kwana biyu wajen kawo sulhu a tsakanin kabilun biyu. Ya ce wadannan irin fadace-fadacen kabilanci sun fi shekara 10 ana yin su kuma hakan na kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro.

ADVERTISEMENT

“Wadannan kabilu biyu sun zauna tare da juna tsawon shekaru amma a bara fada ya barke a tsakaninsu har sau uku wadanda suka haddasa asarar rayuka. Amma a fadan da suka yi mun yi nasarar raba fadan sannan mun yi nasarar kama 71 daga cikinsu,” inji shi.

A lokacin da yake mika wadanda ake zargin ga ’yan sandan, Janar Bello ya umarci ’yan sandan su dage wajen gudanar da bincike domin gano ainihin wadanda ke da hannu a haddasa fadace-fadacen. Ya ce dole ne a aiwatar da bincike a tsakanin wadanda aka kame domin mafi yawancinsu matasa ne wadanda suka karya doka.

ADVERTISEMENT

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Mai kula da Harkokin Ta’addanci da Bincike, Abu Bocho, ya ce yana son a samu zaman lafiya a jihar kafin zaben bana, kuma sojoji da ’yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkin dan Adam.