Da Dumi Dumi

Fadar Shugaban Kasa ta fara fige fika-fikan Osinbajo

Mataimaki Shugaban Qasa Farfesa Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda Shugaba Buhari ya sha kwatwantawa  da mataimaki biyayya, ya samu kansa a tsaka mai wuya bayan da Fadar Shugaban Kasar ta fara fige fika-fikansa inda ta raba shi da shugabancin Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa (EMT) kuma ta karbe ikon sanya ido kan wasu hukumomi da suka hada da Hukumar Bada Tallafin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta Kula da Al’ummun kan Iyakoki (BCDA) da Hukumar Iyakoki ta Kasa (NBC) da kuma Cibiyar Nazarin Bukatun Kasa (NIPSS).

A daren Litinin da ta gabata ce Fadar Shugaban Kasa ta sanar da maye gurbin Kwamitin EMT da Osinbajo ke jagoranta da Majalisar Bada Shawara kan Tattalin Arziki (EAC), inda aka nada Farfesa Doyin Salami a matsayin shugaba. Sauran mambobin kwamitin sun hada da Dokta Mohammed Sagagi, Mataimakin Shugaba da Farfesa Ode Ojowu da Dokta Shehu Yahaya da Dokta Iyabo Masha da Farfesa Chukwuma Soludo da Mista Bismarck Rewane da Dokta Mohammed Adaya Salisu a matsayin Sakatare, kamar yadda Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya sanar.

Majalisar EAC “Za ta rika bada rahoto kai-tsaye ga Shugaban Kasa,” inji shi. Kuma kasa da sa’o’i 24 ne aka janye hukumomin gwamnati da aka ambata a baya daga ofishin Mataimakin Shugaban Kasar, wanda hakan ya haifar da damuwa ga gwamnati da Jam’iyyar APC inda ake zargin ana shirin canja wa wadansu manyan mataimaka na musamman ga Osinbajo zuwa wasu ma’aikatu da cibiyoyi. Wannan ya kara tabbatar da zargin cewa akwai masu son a rage wa Mataimakin Shugaban Kasar karfi ta hanyar karbe cibiyoyin da ke karkashin kulawarsa. Kuma akwai zargin cewa akwai takardar da ake Shugaban Kasar ya fitar yana umarta Mataimakin nasa kan ya rika neman yarjewar Shugaban Kasar kafin aiwatar da ayyukan cibiyoyin da suke karkashin ikonsa.

Sai dai Osinbajo ya musanta cewa akwai baraka a tsakaninsa da Shugaban Kasa. Ya ce cibiyoyin da ke karkashinsa suna aiki bisa doka, kamar Kakakinsa, Laolu Akande ya ce.

ADVERTISEMENT
Share