✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faduwar damina da matsalolin hanya suka sanya tumatir karanci – Sunusi Zarewa

Karancin tumatir ya kunno kai a Jihar Kuros Riba sakamakon rashin kawo shi da masu sayar da shi ke yi daga sassan Arewa. Sai dai…

Karancin tumatir ya kunno kai a Jihar Kuros Riba sakamakon rashin kawo shi da masu sayar da shi ke yi daga sassan Arewa. Sai dai wadansu ’yan asalin jihar na ganin saboda watan azumi da bikin Karamar Sallah ne da Musulmi mazauna jihar masu harkar suka sanya karancin tumaturin a kasuwannin jihar .

Wakilin Aminiya ya zagaya kasuwannin tumatir a Layin Slaughter da ke Kalaba da  Layin Bagobiri a Unguwar Hausawa inda nan ne ake rarraba shi zuwa sauran kasuwannin da ke kananan hukumomin da ke  kusa da babban birnin jihar domin gano dalilan karancin tumatirin.

Alhaji Ibrahim Musa Rawaiya da ke kasuwar tumatir ta Layin Slaughter ya ce “Ba azumi ne ya sanya tumaturin ya yi karanci ba a’a wani lokaci idan damina ta fadi a Arewa dan lambu yana yankewa alhali na gona kuma bai zo ba.”

Shugaban Kasuwar Tumatir ta Jihar Kuros Ribas Alhaji Sunusi Sale Zarewa, ya ce kowane lokaci in damina ta fadi a Arewa masu harkar sayar da  kayan lambu suna tafiya gida su yi noma sannan idan daminar ta fadi wanda ake da shi dan noman rani yana yankewa kuma na damina bai zo ba. Ya ce da ma faduwar damina ce take jawo karancin tumatir don haka sai na gona da aka shuka, ya yi za a debo a kawo a sayar. “Ka ga kuwa dole a dan samu karancinsa a Kudu,” inji shi.

Haka ya ce wani karin dalilin da ke haifar da karancin tumatir, shi ne yadda masu karbar kudin haraji  da jami’an tsaro da suke lura da hanyoyi ke tatsar ’yan kasuwar da ke safarar tumatir daga Arewa zuwa Kudu. “Idan suka dauko  in mutum ya zo shingen jami’an tsaro yanka wa dillalanmu kudi suke yi su ce, sai sun ba su idan kuma ba su ba su ba,  su tsai da motar wato a ajiye ta gefen hanya mutum ne ya dauko kayan lambu a lokacin da yake sauri ya kai kasuwa ya sayar sai a dakatar da motarsa, jinkirin da zai yi kayan za su iya narkewa, wanda hakan zai iya sa mutum ya yi asara kan kudin son zuciya da ake so mutum ya bayar,” inji shi.