✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faduwar Omar al-Bashir

Bayan shafe shekara 30 yan mulkin Sudan Shugaba Omar Hassan al-Bashir mai shekara 75 ya fadi daga kujerar sakamakon shafe wata hudu da al’ummar Sudan…

Bayan shafe shekara 30 yan mulkin Sudan Shugaba Omar Hassan al-Bashir mai shekara 75 ya fadi daga kujerar sakamakon shafe wata hudu da al’ummar Sudan suka yi suna zanga zangar nuna kin jinin gwamnatinsa.

Zanga zangar ta biyo bayan karin farashin burodi, kuma barazanar ballewar rikici da kafa dokar ta-baci da gyare gyaren da Al-Bashir ya yi na daga cikin abubuwan da suka jawo faduwar gwamnatin mutumin da ya mai da kansa tamkar wani Ubangiji a kan alummar kasar Sudan shekara da shekaru.

Omar ya fara aiki a wani kamfanin gine-gine, lokacin yana karamin yaro dan makaranta, sannan ya zama jami’in soja, Omar ya hau karagar mulki ne a wani juyin mulki da ba a zubar da jini ba da sojoji suka hambarar da Firayi Minista Sadik Al-Mahdi a  1989. Domin ganin ya daukaka darajarsa, sai ya kulla kawance da fittaccen malamin nan Hassan Al-Turabi, wanda ya yi fice saboda irin karantarwarsa. Bayan shafe wasu shekaru da samun hadin kan malamin, sai Al-Bashir ya juyawa mutumin da ake ganin shi ne jagoransa a addini baya.

Omar ya hau mulkin kasa mafi girman kasa a Nahiyar Afirka, wacce ta yi fama da yaki kuma ga talauci da ya gagari albarkatun man fetur da ta samu wanda hakan ya kawo ci baya ga kasar. Masu zanga zangar da suka dage wajen hambarar da gwamnatin, sun yi korafin gazawar Al-Bashir a kan rashin samar da ayyukan yi ko ci gaban tattalin arziki da karancin abinci, wadanda suke daga cikin manyan matsalolin da suke damun kasar.

Masu zanga zangar ta lumana sun gudanar da ita duk da irin karfin jami’an tsaron da Shugaba Al- Bashir yake da su, wadanda suka kasance yana kyautata musu tsawon shekaru.Duk da tsarin addini da Al-Bashir yake da shi ya zama tamkar wani gimshikin soja, wanda hakan ya sa  Sudan ta zamo daya daga cikin kasashe masu ’yan sandan jihohi a Nahiyar Afirka.

Al-Bashir ya zama mai fada-a-ji a kasarsa, amma sai dai yana fuskantar matsaloli da kasashen Yamma, inda suke zarginsa da yin alaka da Shugaban Kungiyar Al-ka’ida Osama Bin Laden, sannan ga matsalar rikicin yankin Darfur, wanda sojojin Janjawid suka yi ta kashe bakaken fatar yankin.

Hakazalika kasashen Yamma sun kuma zargi Gwamnatin Al-Bashir a kan mara wa ’yan Janjawid baya, wanda kuma ya musanta hakan, ya kuma bayyana ’yan Janjawid a matsayin ’yan fashi da makami wadanda suka fi karfin gwamnatinsa.Wadannan zarge- zarge su ne aka gabatar gaban Kotun Hukunta Laifuffukan yaki ta duniya a kan Al-Bashir.

Gwamnatin Amurka ta zargi gwamntinsa da daukar nauyin ’yan ta’adda na duniya, kuma ta kakaba wa kasar  takunkumi.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yanke shawarar  ba za ta ba da hadin kai ba wajen mika Al-Bashir gaban kotun.

Lokacin da zanga zangar da ta kifar da Al-Bashir a kan mulki, wadda aka fara a ranar 19 ga watan Disamban bara, gani yake kamar ba za ta yi wani tasiri ba, sai dai lamarin ya fi karfin yadda ake tsammani, in da a ranar 6 ga Afrilu masu zanga zangar suka fita tamkar farin dango, suka mamaye fadar Al-Bashir wadda kuma ita ce hedkwatar sojin Sudan, wannan shi ne ya kawo karshen mulkin Al-Bashir.

Amma dai za a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya sa aka kawo karshen zubar da jinin da aka dade ana yi a tsakanin Sudan ta Kudu.  Ya kuma ba da damar yin kuri’ar jin ra’ayoyin al’umma a kan bai wa al’ummar Sudan ta Kudu ’yanci.

Al-Bashir na daya daga cikin shugabannin Afirka da suka mulki jama’arsu yadda suka ga dama, ya canja tsarin mulkin kasa, domin kasancewa a kan gadon mulki, wadanda irinsu kalilan ne a Nahiyar Afirka a yau, kamar Paul Biya na Kamaru da Yoweri Musabeni na Uganda da Idris Deby na Chadi.

A shekarar 2017 aka hambarar da Robert Mugabe na Zimbabwe a wani juyin mulki na soja. Kawo karshen mulkin Al-Bashir kan iya zama darasi ga shugabannin Afirka na idan shugaba ya kammala wa’adinsa ya sauka lami lafiya. Ganin irin guguwar da ta faru a kasashen Aljeriya da Tunisiya da Masar da kuma Libya, yanzu kuma ga Sudan wannan wata ’manuniya ce, cewa al’umma na da karfi a hannunsu na canja gwamnati ba tare da bindiga ba.