Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Fafaroma na son a kyale a  gina coci a Saudiyya

Fafaroma Francis a tsakiya a birnin Dubai
Fafaroma Francis a tsakiya a birnin Dubai

A karon farko, Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa, a ziyara irinta ta farko a tarihi da wani Fafaroma ya taba kaiwa yankin Larabawa.

Fafaroman ya karbi goyon gayyata ne daga Yarima mai jiran gado na kasar Sheikh Mohammed Bin Zayed Al-Nahyan.

ADVERTISEMENT

Gabanin ziyarar, Fafaroma ya yi kakkausar suka kan yadda ake gudanar da yaki a kasar Yemen, wanda Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga ciki tsundum a karkashin jagorancin Saudiyya.

A wani sakon bidiyo da ya fitar, ya ce “Ina farin cikin wannan dama da Ubangiji ya ba ni domin rubuta wani sabon babi na dangantaka tsakanin addinanmu a kasarku mai albarka.”

ADVERTISEMENT

Ya yaba wa kasar Daular Larabawa, inda ya ce “kasa ce mai kokarin kawo daidaito wajen zamantakewar al’umma da ’yan uwantakar dan Adam da kuma zama wata mahada ga mabambantan al’adu da wayewar kawuna.”

Wakilin BBC na Sashin Larabci, Murad Batal Shishani ya ruwaito cewa Fadar Batikan ta nemi a sassauta wa mabiya addinin Kirista hanin gina coci-coci, musamman  a Saudiyya inda aka haramta wa mabiya addinan da ba Musulunci ba gina wuraren ibada kamar yadda BBC ya ruwaito.

Fafaroma Francis ya roki bangarorin da ke yaki a Yemen su tuna da halin da miliyoyin ’yan kasar ke ciki na yunwa da rashi.

Kuma ya ce kukan yaran kasar Yemen ya kai wajen Ubangiji, kuma ya roki bangarorin masu yaki da juna su tabbatar sun kyale tallafin abinci da magani ya isa wurin miliyoyin fafaren hula da yakin ya rutsa da su.

An soki wannan ziyarar ta Fafaroman zuwa Abu Dhabi ganin cewa dakarun Hadaddiyar Daular Larabawa na mara wa bangaren gwamnatin Yemen a yakin da take yi da ’yan tawayen Hothi.

Amma ya kare kansa, inda ya ce wannan ziyarar zuwa wurin da ya kira mahaifar Musulunci dama ce ta zurfafa dangantaka a tsakanin manyan addinan duniya biyu – wato Musulunci da Kiristanci kamar yadda BBC ta ruwaito.