Da Dumi Dumi

Fafutikar kafa masarautar Burumawa (2)

A makon jiya muka kawo kashi na farko na wannan mukala game da Masarautar Burumawa da ke Jihar Filato, to yau cikin ikon Allah mun kawo kashi na biyu kuma na karshe kamar haka:

Taron ’yan jarida na duniya

A ranar 15 ga Afrilun 1986, al’ummar Burumawa suka gudanar da taron ’yan jarida a garin Jos, taron da ya samu halartar wakilan jaridu da gidajen rediyo da dama ciki har da na ƙasashen waje.

Bayan karanta tarkardar bayan taro da Mista Sallah Dashe ya yi a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Burumawa, jawabin ya samu yayatawar jaridu sosai ciki har da gidan rediyon Jihar Filato da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ke Jos da sauransu.

Bayan faruwar waɗannan al’amura, sai Masarautar Kanam ta hanzarta mayar da martani game da wancan jawabin Mista Sallah, ita kuma gwamnatin Filato a nata ɓangare ta dakatar da filin Burumwa mai suna Bogghom Magazine da ake gudanarwa a gidan rediyon jihar da ke garin Jos. Wannan shiri, na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake jin muryar Burumawa. Haka nan cin zarafin da jami’an tsaron Karamar Hukumar Kanam ke yi wa Burumawa ya ci gaba.

ADVERTISEMENT

Ƙawancen Burumawa da Jarawa

Wannan cin zarafi da ake yi wa Burumawa, ya saka sun samu tausayawa da goyon baya daga wasu kabilun jihar ta Filato, mafi muhimmanci daga ciki ita ce kabilar Jarawa, kasancewar ita ma ta fuskanci irin wannan matsin lamba kafin su samu nasarar kafa tasu masarautar a1983.

Wannan tausayawa ta Jarawa, ta kai har ga an kafa ƙungiyar haɗin gwiwa tsakanin Burumawa da Jarawa, wacce ake sassauya shugabancinta a tsakanin ƙabilun biyu tun daga wancan lokacin har zuwa yau.

Shigowar gwamnati cikin lamarin

Duk wannan balahira da ake yi wa Burumawa ta gudana ce a zamanin gwamnatin Kanar M.C. Alli, mutumin da ake zargi da ra’ayin rarraba kan ƙabilun Jihar Filato. Ana tsakiyar wannan hali, sai Allah Ya kawo sauyin gwamnati, aka ɗauke Kanar Alli daga Jihar Filato, aka kawo Kanar Lawrance Onoja a watan Agustan 1986, wanda shi kuma yake da ra’ayin haɗa kan ƙabilun jihar ta Filato tare da gudanar da jagorancinsa bisa daidaito a tsakanin jama’a.

Gwamnatin Onoja, ta gayyaci sassan biyu; Sarkin Kanam da ayarinsa da kuma Burumawa a ɗaya gefen zuwa taron sasantawa a ofishin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.

An fara gudanar da wannan taro a garin Jos, a ofishin Kwamishinan, har an saurari jawabin Burumawa, ɗaya ɓangaren ya fara ba da nasa jawabin sai musu ya kaure. Hakan na faruwa, jami’an tsaron farin kaya suka gaggauta sanar da Gwamna wanda shi kuma nan take ya yi umarnin cewa taron ya koma ofishinsa. Wanda kuma hakan aka yi, aka wakilta mutum uku-uku daga kowane ɓangare, suka rankaya tare da Kwamishinan zuwa Ofishin Gwamnan.

Da isarsu Ofishin Gwamna, sai ya ji ta bakin Sarkin Kanam. Bayan ya gama nasa jawabi, sai Gwamnan ya ce, gaskiyar lamari, yana zargin Sarki da rura wutar wannan rikici, kuma shi Gwamna yana ɗora alhakin faruwar wani abu nan gaba a kan Sarkin Kanam. Sannan ya ja wa Sarkin kunne cewa, shi gwamnatinsa ba za ta yarda da irin wannan ba. Daga ƙarshe ya sallami ayarin bisa alƙawarin cewa, zai waiwaiyi maganar a lokacin da ya dace.

Tabbas Gwamna Onoja, ya yayyafa wa wutar ruwa, kuma ta lafa. Sannan ya mutumta Burumawa, domin ya yi wa ɗansu Baburme muƙamin Babban Sakatare, daga baya kuma Kwamishina, wanda shi ne muƙami mafi girma da Baburme ya riƙe a tsawon tarihin Jihar Filato, a karon farko, a wancan lokaci.

Bayan tafiyar Onoja, sai aka maye gurbinsa da Kanar Habibu Shu’aibu (1996 -1998), wanda shi kuma Bakano ne. Shi ma ya ɗora daga inda Onoja ya tsaya, har ta kai shi ga kafa kwamitin da ya waiwaiyi buƙatar kafa masarautu. Kwamitin da ya ba shi rahoton buƙatar yin haka, shi kuma ya amince. Shirye-shirye suka yi nisa, ana gab da aiwatar da shirin sai Sarkin Kanam ya garzaya Kano, ya kama ƙafar  Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, shi kuma ya tuntuɓi Kanar Habibu, inda a ƙarshe aka yi fatali da maganar kafa masarautar.

Yunƙurin kisa

Da abubuwa suka zafafa, an zargi Masarautar Kanam da shirya kisa, inda ake zargin ta tsara za ta kashe wadansu idon garin tafiyar, ciki har da Alhaji Shehu Suleiman.

Masarautar ta yi amfani da rigingimun da suka faru a shekarar 2000 wajen kashe Mista J.T. Nimfa, Baburme a gidan gonarsa a ƙauyen Kyamsangi tare da ƙona gidansa da ke Dengi, wanda a cikin wannan gida ake gudanar da tarurrukan fafutikar.

Gari na wayewa, ranar Juma’a, Alhaji Shehu Suleiman ya fito daga gidansa domin tafiya Dengi, sai ya yi kiciɓis da makasa, makiyaya, sun tsaya da baburansu a bayan gidansa, suka tare shi, suka sanar da shi saƙon da suke tafe da shi da kuma wanda ya ba su saƙon. Alhaji Shehu ya rantse musu da Allah cewa, bai takawa kowa ba, ballantana ya zubar, saboda haka yana tare da Allah, babu abin da zai faru da shi sai alheri.

Nan take waɗannan makasa suka fara harbin Alhaji Shehu. Sai da suka harbe shi sau uku bindigar ta ƙi tashi. Suka yi wa bindiga fitsari, ta ƙi tashi. Daga ƙarshe sai suka ce, za su binciki gidansa, wai sun samu labari ya ajiye ’yan ta’adda, kuma babban ɗansa da ke aiki a Legas ya aiko masa da makamai.

Ana cikin wannan hali ne, sai wani jami’in tsaro na farin kaya na Karamar Hukumar Kanam ya bayyana, ya gayyaci Alhaji Shehu zuwa ofishinsu. Bayan da suka sallame shi, sai ya tafi fadar Kanam domin bin bahasi, amma fir, aka nuna rashin masaniyarsu kan faruwar lamarin, kuma suka nuna masa cewa, ya bar abin a hannun Allah. Tun daga wannan rana har zuwa yau, ba amo-ba-labarin Mista Ninfa, ballatana a yi maganar kama waɗanda suka yi aika-aikar.

Haƙa ta cimma ruwa

A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2002, Gwamnan Jihar Filato Mista Joshua Chibi Dariye ya shelanta kafa Masarautar Burum, tare da ƙarin wasu masarautu guda goma. Wannan ci gaba da Burumawa suka samu, bai yi wa sarakunan Kanam daɗi ba. Saboda haka suka gudanar da taron ’yan jarida suka soki wannan ci gaba da cewa, an ƙirƙiri Masarautar Burum ce kawai domin a daɗaɗa wa wadansu ’yan tsirarun Kiristoci rai. Ba tare da jinkiri ba, Ƙungiyar Ci gaban Burumawa ta mayar da martani da cewa, dagatan Burumawa 14 daga cikin 16 da suka zaɓin sabon Sarkin Sabuwar Masarautar Burum duk Musulmi ne. Haka kuma shi kansa Sarkin da aka zaɓa; Pankwal Bogghom, Alhaji Shehu Sueliman Musulmi ne. Saboda haka wannan suka ne kawai marar dalili.

Daga ƙarshe, bayan duk jinkirin da aka samu daga ɓangaren gwamnati da kuma zagon-ƙasa mai zafi daga ɓangaren Masarautar Kanam, babban ɗan Sarki Shehu Suleiman ya yiwo takakkiya daga Bienna ta ƙasar Austireliya, ya samu Gwamna Dariye, ya roƙe shi aka tabbatar da kafuwar wannan masarauta tare da naɗa mahaifinsa Alhaji Shehu Sueliman a matsayin Sarkin Masarautar Burumawa na farko, Mai Daraja ta Biyu, haɗe da naɗin jikan Sarkin Kanam Alhaji Muhammadu Mu’azu Muhammadu II, a matsayin sabon Sarkin Kanam, sakamakon rasuwar kakansa Alhaji Muhammadu Ibrahim.

Tsohon Sarkin ya rasu a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2005. An kuma yi waɗannan naɗe-naɗe biyu a ranar 9 ga watan Afrilun 2005, zamanin Gwamnan Jihar  Filato, Joshua Chibi Dariye.

Ta-leƙo-ta-koma

Bayan ƙarewar wa’adin mulkin Dariye a matsayin Gwamnan Jihar Filato, sai aka zaɓi Mista Jonah Jang a matsayin Gwamna a ƙarƙashin jama’iyya guda, wato PDP. Shigar Jonah Jang ofis ke da wuya, sai ya dakatar da dukkan waɗancan masarautu da Dariye ya ƙirƙiro, a shekarar 2007, wanda wannan ya shafi Masarautar Burum, tare da Sarkinta Alhaji Shehu Suleiman, Pankwal Bogghom.

Shigar da kara

Gazawar gwamnatin Jonah Jang wajen maido da waɗannan masaratu da ta dakatar, ya wajabta wa Ƙungiyar Ci gaban Burumawa da haɗin gwiwar Alhaji Shehu Suleiman zuwa kotu, domin neman kotu ta maido da wannan masarauta tare da sarkinta karagar mulki haɗe da biyansa albashinsa tun daga ranar da aka dakatar da masarautar har zuwa ranar da za a mayar da shi. An shigar da wannan ƙara a Babbar Kotun Jihar Filato.

A ƙarshe alƙalin kotun, ya yanke hukuncin cewa, lallai Gwamnatin Filato ta mayar da wannan masarauta ta Burum tare da Sarkinta Alhaji Shehu Suleiman kan kujerarsa haɗe da biyansa albashi na tsawon lokacin da ya yi a dakace, kamar yadda suka nema a cikin takardar ƙarar. Amma, fir, gwamna Jang, ya ƙi mutunta wannan umarni na kotu.

Maido da Masarautar Burum da Sarkinta

Zamani goma Sarki goma. Kafa sabuwar gwamnati a Filato, a ƙarƙashin Gwamna Simon Baƙo Lalong a shekarar 2015, sai ya sake bai wa Masarautar Burum damar komawa gidanta na tsamiya tare da sarkinta, Alhaji Shehu Suleiman.

Tun farko, babban ɗan Sarkin Burum, ya je ya yi wa Gwamna Lalong murnar ɗarewa wannan babbar kujera mafi girma a faɗin wannan jiha ta Filato. Bayan gama yi masa murna sai ya shigar da buƙatar waiwaiyar umarnin da Babbar Kotun Jihar ta bai wa gwamnati mai barin gado amma ta ƙi bi, game da mayar da Masarautar Burum da kuma Sarkinta kan kujerarsa. Bayan ya gama, sai shi sabon Gwamnan ya amsa da cewa, zai duba lamarin da idon rahama.

Kwanci-tashi, har aka samu shekara biyu da yin waccan magana, saboda haka sai wannan ɗa na Alhaji Shehu ya sake komawa wajen Gwamna a wannan karon, sai ya tafi masa da takardar koke daga Ƙungiyar Ci gaban Burumawa wadda ta nemi a mutunta wancan umarni na Babbar Kotu, haɗe da kwafin umarnin, da ke ɗauke da kwanan wata, 2 ga Janairun 2017. Saboda haka nan take Gwamnan ya amshi wannan buƙata. Ya mayar da wannan masarauta da sarkinta tare da cika dukkan sharruɗan da kotun ta buƙaci a yi. An sake kafa wannan masarauta da Sarkin nata a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2017.

Bayan wannan kuma, Gwamnan ya samu halartar bikin raya al’adun Burumawa, abin da ya sa dangantarsa da Burumawa ta ƙarafafa, har ta kai ga an ba shi sarautar Jarumin Bogghom.

Wannan shi ne abin da ya gudana, sannan kuma ya zama sanadin kashe bakin wutar fafutikar da aka ƙyasta ashanarta ta riƙa ci tsawon shekara 35 (daga 1982 – 2017).

Mun kammala

Share