✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalar  Kwana Goma na farkon Zul-Hajji

Sheikh Abu Usman Nahadi ya ce magabata bayin Allah salihai suna girmama kwanaki goma, guda uku (1) Goma ta daya ita ce Goman Karshen watan…

Sheikh Abu Usman Nahadi ya ce magabata bayin Allah salihai suna girmama kwanaki goma, guda uku

(1) Goma ta daya ita ce Goman Karshen watan Ramadan

(2) Goma ta biyu ita ce Goman Farkon  watan Zul-Hajji

(3) Goma ta uku ita ce Goman Farko ta watan Almuharram wato watan farkon shekarar Musulunci

Dalili na goman karshe a watan Ramadan shi ne a cikinsa ne aka yi Daren Lailatul Kadiri, wanda Allah Yake cewa a cikin Alkur’ani Mai girma;

“(1) Hakika Mu muka saukar da shi (Alkur’ani) a cikin Dare Mai Alkadari,

(2) Me ya sanar da kai mene ne Dare Mai Alkadari?

(3) Dare Mai Alkadari ya fi wata dubu.

(4) Mala’iku da Ruhu (Mala’ika Jibrilu AS) suna sauka a cikinsa da dukan  al’amura da izinin Ubangijinsu.

(5) Aminci ne shi daren (kalmar da suke ta fada) har zuwa hudowar alfijir.”

Ita kuma goma ta biyu akwai aikin Hajji akwai Arafa. Dalili kuwa Allah Yana cewa a cikin Suratul Hajji aya ta 27-28 da kuma Suratul Bakara aya ta 198.

Suratul Hajji Aya ta 27 da 28: “Kuma ka yi shela a cikin mutane saboda yin Hajji, za so zo maka matafiya a kasa da kuma kan kowanne rakumi za su zo maka daga kowane lungu mai nisa Don su halarci amfanin da za su samu kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Muka arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (wato rakuma da tumaki da shanu ), sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci.”

Suratul Bakara Aya ta 198: “Babu laifi a kanku ku nemi falala daga Ubangijinku (wato ku nemi arziki ta hanya saye da sayarwa) idan kuwa kuka koma daga Arafa sai ku yi ta ambaton Allah a daidai Masha’aril-Haram (ta yin hailala da kabbara da hamdala), ku tuna Shi kamar yadda Ya shiryar da ku (ga ayyukan hajjinku da sauran ayyakan addininku) koda yake ku kasance da can kafin (shiriyar) cikin batattu.”

Na uku kuma ita ce Ranar Ashura ranar babbar nasara ga Annabi Musa (AS) wato a watan Almuharram ne wannan rana ita ce ranar da Allah Ya hallakar da Fir’auna da jama’arsa. Dalili kuwa Allah Yana cewa a cikin Alkur’ani Suratul Daha aya ta 77-79:

“Hakika Mun yi wa Musa wahayi cewa ka tafi da bayiNa cikin dare sannan ka keta musu hanya kekasasshiya cikin kogi ba za ka ji tsoron riskar(Fir’auna da jama’arsa) ba, kuma ba za ka ji tsoron (nutsewa)ba.  Sannan Fir’auna ya bi su, shi da rundunarsa sai kogin ya hade da su suka nutse kakaf.Fir’auna kuma ya batar da mutanensa bai kuma shiyar da su ba.”

Yanzu bayanin da za mu yi shi ne a kan Goman Farko na watan Zul-Hajji saboda ana zaton ranar Asabar mai zuwa ce 1 ga watan Zul-Hajji (wato 1-12-1440 Bayan Hijira) wadda ta yi daidai da 3 ga Agustan 2019.

Goma na Farko ga Zul-Hajji, ayoyi da yawa sun yi magana a kansu (Allah Yana cewa a cikin  Suratul Hajji Aya ta (28):

“(28) Don su halarci amfanin da za su samu kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sannanu a kan abin da Muka arzuta su da shi na dabbobin ni’ima ( wato rakuma da tumaki da shanu), sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci.” Kwanakin nan su ne kwana 10 ga watan Zul-Hajji, don Allah Yana cewa a cikin Suratul Fajari, Aya ta 1-2:

“(1) Ina rantsuwa da alfijir

(2) Da darare goma.”

Darare goman nan su ne ake nufi da kwanaki goma na watan Zul-Hajji kuma kuma kamar yadda ayoyi sun tabbatar da muhimmancin  wadannan kwanaki haka Sunnah ta tabbatar da falalarsu. An samu Hadisi daga Dan Abbas (RA) Allah ya yarda daga Manzon Allah (SAW) ya ce “Babu wani irin aiki da ya fi soyuwa a wurin Allah  kamar yin alheri a wadannan kwanaki goma na Zul-Hajji. Sai  sahabbai suka ce har da fita jihadi bai kai ladan wadannan kwanakin ba? Sai Annabi (SAW ) ya ce “Eh har fita jihadi bai kai ladan wadannan kwanaki ba, sai dai idan mutum ya fita jihadi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba shi ne kawai ya fi lada.” Imam Buhari ne ya fitar da Hadisin. An samo Hadisi daga Dan Umar (RA), ya ce “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wata rana da ta fi girma a wajen Allah kuma Ya fi so kuma aiki mai kyau ya fi lada a cikinsu kamar kwanaki goma na Zul-Hajj. (Don haka ne Annabi ya ce) ku yawaita fadin la’ilaha illallah wal hamdulilah wallahu akbar.” Imam Dabarani da Baihaki suka fitar da Hadisi.

Malamai sun ce:

(1) Dalilin fifikon wadannan kwanaki goma shi ne akwai Sallar Idi a cikinsu  sannan akwai azumi guda tara da ake so mutum ya yi  tun daga 1 ga wata har zuwa 9 ga wata, wato azumin Ranar Arafa da kuma Layya da ake yi da kuma hadaya, da shi kansa aikin Hajji duk a wadannan kwanaki a ke yin su . Hafiz ya fadi wannan a cikin Litaffinsa Fathul Bari.

(2) A ciki ake samun Ranar Arafa wadda a cikinta ne Allah Ya cika ni’imominSa kuma a ciki ne aka cika muku addininku na Musulunci.  An rawaito daga Umar (RA)  wani Bayahude ya ce “Ya Shugaban Muminai kuna karanta wata aya a cikin littafinku da mu ne Yahudu da mun mayar da wannan rana ta zama Ranar Idi.” Sai Sayyidina Umar  (RA) ya ce masa wacce aya ce sai ya ce masa  ciki Suratul Ma’ida, Aya ta uku.

“(3) A yau Na cika muku addininku, Na kuma cika ni’imaTa a gare ku, Na kuma zabar muku addinin Musulunci (shi ne ) addini (na gaskiya).” Sai Sayyidina Umar ya ce masa ai mun san ranar da ta sauka mun san kuma lokacin da ta sauka ranar da ta sauka ranar Juma’a ce a lokacin da Annabi (SAW) yake tsaye a Arafa ne.” Imam Buhari ne ya fitar da Hadisin

(4) A cikinta ce aka samu rana babba da ake kira Ranar Hajjil Akbar. An ruwaito  daga Dan Umar (RA) ya ce Manzon Allah (SAW) su tabbata a gare shi ya ce “Ranar Hajji Babba ita ce Ranar Yanka wato Ranar 10 ga watan Zul-Hajji.  Abu dawud da Ibn Maja ne suka fitar da wannan Hadisi. Wadannan dalilai ne da ake  gani duk wanda Allah Ya ba shi  damar halartar wadannan kwanaki  a kasarsa yake wato Najeriya ko a wata kasa to ya yi kokari ya amfana da wadannan kwanaki masu zuwa. Zai iya amfanuwa ta wadannan hanyoyi guda bakwai

(1) Ko ya tafi Makka don yin aikin Hajji da Umara a cikin wadannan kwanaki shi ne ma abin da ya fi idan yana da hali. Don Annabi (SAW) ya ce “Wanda ya yi Umara zuwa wata Umara to kaffara ce ta zunubansa a tsakaninsu, shi kuma aikin Hajji mai kyau ba ya da sakamako sai Aljanna.” Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.  Manzon  Allah (SAW) ya ce “Wanda ya yi aikin Hajji bai sadu da iyalinsa ba kuma bai aikata wani laifi na fasikanci ba, to zai dawo kamar yau mahaifiyarsa  ta haife shi.” Buhari da Muslim ne suka ruwaito. Kuma Annabi (SAW) ya ce, “Ku yi Hajji ku yi Umara domin suna kore talauci da zunubi kamar yadda makeri yake kera wani abu daga bakin karfe ko zinare ko azurfa ya fita kalkal yana kyalli.”

(2) Yin azumi tara ko abin da ya sawwaka, za ka iya yi ko da guda daya  ne na Ranar Arafa. Ummu Salma da Hafsa (Allah Ya yarda da su), sun ruwaito cewa Annabi (SAW)ya kasance yana azumin 9 da watan Zul-Hajji sai dai idan yana aikin Hajji, to ba ya azumi Ranar Arafa.  Abu Dawud da Nisa’i da Ahmad ne suka fitar da wannan Hadisi. Abu Huraira ya ruwaito daga Annabi (SAW) ya ce ba wata rana da ta fi soyuwa a wajen Allah (a bauta maSa a cikinta) kamar ranar goma  ga watan Zul-Hajji, (koda da  azumi daya ne a cikinta yana daidai da ladar shekara guda  kowace nafila da aka yi a cikinsu yana daidai da nafilar da ake yi a Daren Lailatul Kadiri. Tirmizi ya ruwaito.Daga Abu Kattada (RA) daga Annabi (SAW) ya ce “Yana kyautata zaton Allah zai kankare wa mutum  zunubansa na shekara biyu na bara da na bana.” Malaman Hadisi biyar ne suka ruwaito Hadisin amma ban da Buhari. Wadannan hadisai suna nuna falalar kwanaki goma  na Zul-Hajji

SP Imam Ahmad Adam Kutubi, Zone 7 Police Headkuater’s, Abuja 08036095723