✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalar zikiri (3)

Zikiri ko ambato da tuna Allah yana kasancewa da harshe ko da aiki. Domin Allah Yana cewa: “Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni.”…

Zikiri ko ambato da tuna Allah yana kasancewa da harshe ko da aiki. Domin Allah Yana cewa: “Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni.” (daha:14). Da  fadinSa: “Wadanda suka yi imani, zukatansu suna (samun) natsuwa ne da ambaton Allah. Ku saurara! Da ambaton Allah zukata suke samun natsuwa.” (Ra’ad: 28). Ambaton Allah  yana korar Shaidan ya katange mutum daga aikata barna. Annabi (SAW) ya ce: “Kuma ina umartarku da ambaton Allah, domin misalin hakan shi ne (kamar) wanda makiyi ya fito nemansa yana mai sauri, sai ya fake a bayan katangar da za ta boye shi, sai Allah Ya hana shi (abokin gabar) daga isa gare shi.” Don haka Musulmin da yake yawan ambaton Allah, yana fakewa ne a wurin Allah a koyaushe, yana sanya Allah Ya zama katanga gare shi daga makiyansa kuma Ya katange shi daga azabar wuta da dukan abubuwan ki.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi falalar addu’ar ita ce addu’ar Arfa. Kuma mafi alherin abin da na ce ni da Annabawan da suka gabace ni shi ne” La’ilaha illallahu wahadahu lasharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir.” Wannan jumla tana daga cikin mafiya falalar zikiri kuma mafiya girman zikiri, kalma ce mai sauki da ba ta daukar lokaci mai yawa a rayuwar Musulmi, amma tana da falala mai girma, ga wanda ya san ta ya san ma’anarta da abubuwan da ta kunsa.

Karatun Alkur’ani zikiri ne hailala da tasbihi da wa’azi da daukar ilimi zikiri ne.

Zikiri ya shafi kowane aiki na Musulmi, shi ne ruhin kyawawan ayyuka, wannan ya sa Allah Ya yi umarni a tuna da Shi a ambace Shi bayan idar da salloli. “Sa’annan idan kuka kare Sallah, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sansaninku (kwance ko kishingide).” Nisa’i: 103). Allah Mai girma Ya yi umarni a ambace Shi a yi zikirinSa a bayan idar da sallolin farilla mutum ya dauwama yana ambaton Allah a cikin masallaci ko a wajen masallaci. Ya ce: “Sa’annan idan an kare Sallah, sai ku watsu a bayan kasa kuma ku nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci sunan Allah da yawa, tsammaninku, ku samu babban rabo.” (Jumu’a: 10). Musulmi ya rika tuna Allah yana yawan ambatonSa hatta a lokacin da ya fita neman abinci.

An hana mu shagalta da dukiya da ’ya’ya su zamo sun hana mu ambaton Allah. Allah Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada dukiyoyinku da ’ya’yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya aikata haka, to, wadannan su ne masu hasara.” (Munafikun: 9). Ke nan babu wani lokaci da aka yarje wa Musulmi ya shagaltu da wani abin duniya har ya mantar da shi ambaton Allah. Game da masallatai Allah Ya ce: “A cikin wadansu gidaje wadanda Allah Ya yi umarnin a daukaka, kuma a ambaci SunanSa a cikinsu, suna yin tasbihi a gare Shi a cikinsu safe da maraice. Wadansu maza, wadanda wani fatauci ba ya shagaltar da su kuma sayarwa ba ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsayar da Sallah da bayar da zakka suna tsoron wani yini wanda zukata da gannai suna bibbirkita a cikinsa. Domin Allah Ya saka musu da mafi kyan abin da suka aikata, kuma Allah Ya kara musu daga falalarSa. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so ba da lissafi ba.” (Nur: 36-38).

Don haka ku yawaita ambaton Allah a kowane lokaci da hali, ku ambaci Allah kuna tafe ko a zaune. Ku ambaci Allah a cikin shagunanku da wuraren ayyukanku. Ku ambaci Allah a inda kuke taruwa, ku ambaci Allah a cikin gidajenku kowane domin Allah Ya haskaka zukatanku Ya kyautata ayyukanku.

Kada wani Musulmi ya dauka ana zikiri ko ambaton Allah ne kawai a wani kebantaccen wuri ko lokaci ko sai wani ya ba ka zikirin ko ya lizimta maka. Allah Ya riga Ya lizimta maka zikiri, ManzonSa (SAW) kuma ya koya maka yadda ake yi. Ka yi kokarin gwamutsar malamai su karantar da kai Alkur’ani da sauran azkar don ka san yadda ake yi tare da sanin ma’anoninsu domin ya zamo kana yin zikirin a kan fahimta da sanin abin da kake yi.   

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ce: “La’ilaha illallahu wahdahu lasharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir” a yini sau dari, zai kasance masa ’yantar da wuya goma,” ma’ana kamar ya ’yanta bayi goma. Shi ke nan? Sai ya ce: “Kuma za a rubuta masa lada dari” Iyakarsa ke nan? Sai (SAW) ya ce: “Kuma za a shafe masa zunubai dari.” Daga nan fa? “Kuma za ta kasance masa hirzi (tsaro) daga Shaidan a wannan yini nasa har ya yi yammaci.” An gama ke nan? “Kuma babu wani mutum da zai zo da abin da ya zo da shi, sai wanda ya yi abin da ya fi nasa yawa!”

Tsarki ya tabbata ga Allah! Wannan garabasa ta kai garabasa, dubi darajar da za a ba mai zikiri kan kalmomi masu saukin fadi. Kai a wani Hadisin, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ce: “Subhanallahi wa bihamdihi a yini sau dari za a shafe laifuffukansa ko da sun kai misalin kumfar teku!” 

Har wa yau Manzon Allah (SAW) yana cewa: “In fadi: “Subhanallahi wal hamdu lillahi wa la ilaha illallahu wallahu akbar,” ya fiye min dadi daga duk abin da rana ta bulla a kansa.” Buhari ya ruwaito daga Abu Huraira (RA).

Mene ne rana take bulla a kansa? Shi ne wannan duniya da muke ciki, wadannan kalmomi sun fi dukiya da taskokin da suke cikinta, sun fi kasashe da jiragen ruwa da na sama da duk wani alatu da ke cikinta alheri a wurin Allah sun fi su kuma daraja da mukami.

Sannan duk inda ake ambaton Allah mala’iku suna zama a wurin kamar yadda Allah Ya shaida wa Annabi (SAW) cikin Hadisin kudusi: “Lallai Allah Yana da mala’iku da suke kewaya hanyoyi suna neman masu zikiri. Idan suka samu wadansu mutane suna ambaton Allah, sai su yi kira cewa: Ku zo ga abin da kuke nema, sai su lullube su da fika-fikansu har zuwa saman duniya. Ya ce: Sai Ubangijinsu Ya tambaye su, alhali shi ne Mafi sani daga gare su: “Me bayiNa suke cewa?” Ya ce: Sai su ce: Suna yi maka tasbihi suna yi maKa takbiri da tahmidi da tamjidi. Sai Ya ce: Shin sun gan Ni ne? Ya ce: Sai su ce: A’a ba su gan Ka ba. Sai Ya ce: ‘Yaya da a ce sun gan Ni? Ya ce: Sai su ce: Da sun gan Ka da sun fi tsananin bauta maKa da sun fi tsananin girmama Ka da sun fi tsananin yi maKa tasbihi! Ya ce: Sai Ya ce: To me suke roko daga wuriNa? Sai su ce: Suna rokonKa Aljanna. Sai Ya ce: “Sun gan ta ce? Sai su ce: A’a wallahi ya Ubangiji ba su gan ta ba! Sai Ya ce: “To da sun gan ta fa? Sai su ce: Da sun gan ta da sun kasance mafiya tsanani ga kwadayin nemanta da sun fi girman son ta. Sai Ya ce: Kuma a kan me suke neman tsari? Sai su ce: Suna neman tsari daga wuta. Sai Ya ce: Shin sun gan ta ce? Sai su ce: A’a wallahi ya Ubangiji ba su gan ta ba! Sai Ya ce: “To yaya in da a ce sun gan ta? Sai su ce: Da sun gan ta da sun kasance mafiya tsananin gudu daga gare ta, da tsananin tsoro daga gare ta. Ya ce: Sai ya ce: “To ina shaidar da ku cewa lallai Ni na gafarta musu.” Sai wani mala’ika daga cikin mala’iku ya ce: “A cikinsu fa akwai wane ba ya tare da su, ya zo ne saboda wata bukata – zai wuce zuwa wani wuri sai ya gan su ya zauna tare da su ba da niyyar musharaka da su a wannan wurin zama ba. Sai (Allah) Ya ce: “Ai su masu zama ne da duk wanda ya zauna da su ba zai tabe ba.”