Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Falalu Dorayi ya gargadi mutane kan yada labarin karya

Falalu Dorayi
Falalu Dorayi

Fitaccen darakta Falalu Dorayi ya bukaci mutane su rika tabbatar da ingancin labarai kafin yada su a baki ko ta kafar sadarwa da ake kira soshiyal mediya.

Daraktan wanda yake fitowa a fina-finai ya yi nasihar ce a shafinsa na Instagram a ranar Asabar da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ka tabbatar da ingancin labari kafin ka yada shi ta hanyar fada da baki ko a soshiyal mediya. Mai neman tsira da mutunci duniya da Lahira shi ne mai kiyaye irin labaran da zai rika isarwa ga mutane, musamman a wannan lokaci na siyasa da zantukan karya da kage su ne mafi yawa a labaran da muke karantawa.”

Daraktan ya ce Ubangiji (SWT) Ya yi kira da wadanda suka yi imani cewa idan wani fasiki ya zo da labari to su nemi bayani don kada wadansu mutane su cutu.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ubangiji (SWT) Ya ce, “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan fasiki ya zo muku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuma masu nadama.”

Falalu Dorayi ya nanata cewa duk abin da bawa zai fadi to Allah Ya ajiye masa mala’iku da suke rubutawa, inda dole ne kowa sai ya karanta littafinsa ranar Alkiyama,

Darakta ya ce, Ubangiji Ya yi umranin cewa “Kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lallai ne ji da gani da zuciya, dukan wadancan (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya.”