✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fancon fincikar ficikar facaka

Fafutikar farautar faske -faske Fuffukar fuka-fukin fake Fetsarar fike-fike Firi-firin faskare feke-feke Fantamawar fankamar fanke   Janjanin jinjinar jarirai Janjamin jimamin jan-rai Jaye-jayen jan birai…

Fafutikar farautar faske -faske

Fuffukar fuka-fukin fake

Fetsarar fike-fike

Firi-firin faskare feke-feke

Fantamawar fankamar fanke

 

Janjanin jinjinar jarirai

Janjamin jimamin jan-rai

Jaye-jayen jan birai

Jijjigar takarkarai

Jogane-joganen ja’irai

 

Gwamna gwarangwam

Gararuma gararam

Gingimeme giririm

Gundumar gudun gangame gam

Gararam gigigim gum

 

Tsofafin ’yan kwadago

Cikinku gwamnoni aka hango

Sani-atta da wakilan rafkiya an tattago

Kumbiya-kumbiya suke a kango

Sun tura talaka ya kai bango

 

Kurmushe-kurmushen kurmusu

Samarin-kusu

masu tufka da warwarar musu

’Yanmatan jaba da gafiya na bula asusu

Munin lakabinku na cikin kamusu

 

Wai dandani haukaci

Kakarin ka-ci-ci-ka-ci-ci

Miyagu masu munafunci

Na jefa jama’a kunci

Wawaye nai musu tumasanci

 

Zaman kashe fatari

Al’umma na watangaririyar garari

Mai ingarma kan kuturi

Mugu zaune  yana fariyar fahari

Al’umma na watangaririyar garari

 

Ka ji ’yan watanda

Nanuguniya calkako wahanda

Cilkowa tsuntsun watanda

Toyayyar masa a tanda

A tutulo ruwa daga randa

 

Fatarsa ta ganda

Busasshen kifi na banda

Far-far-da-ganda

Kurararin karsashin karkanda

Kaftun kartar kasar fadin kadada

 

Da alkalamin sara suke tasu ta’ada

Illarsu tai kama da tada kan adda

Ragargazar romon rabashen ragagada

Sani-atta ya sungumi sanda

Dumuiniyarsa dandinsu ta zarta Uganda

 

An ce sun ziyarci Ruwanda

Sui ta gada-gadar gudun gada

Talaka na dandana kuda

Manyan kwabo na ta rangada guda

Da harkallar harigidon hada-hada

 

An ga rawar Saurayin-kirinki

Dan samari marar kirki

Al’umma na ta fafutikar abin girki

Miyagu nai musu kaki

Sun gaza furta uffan da baki

 

Kasar nan akwai su kowane yanki

Tattalin dukiya sun maishe shi masaki

Sun maishe da kowa musaki

Su kuwa sui dabgen naman awaki

Lamurransu na da ban mamaki

 

In kai magana a ce ka fiye raki

Ana ganinsu sui ta laftun mangalar jaki

In sun sauke su boye a daki

Wasu su difara muku garin kwaki

Su zo sui ta durfafar darkaki

 

Fancon fako

Fankon makoko

Fetsarar yin sako

Fafatawar masu yawo da koko

Fashe-fashen kunshin sako

 

Ku ne dai kuka nace

Tuni su sun dace

Da suka dafe sai suka bace

Dararraku sun kece

Sun barku da ka-ce-na-ce

 

Wa-ka-ci-ka-tashi

Halin bera ba fashi

Har ma sukar mashi

In za ku tashi ku tashi

Su ga fuskoki ba murmushi

 

Mu lallasa su sui laushi

Mu gasa su da garwashi

Su ma su dandani haushi

Jikkunansu sui yaushi

Shi ke nan ba bashi

 

Sai a zo ai sasanci

Miyagu su tuba da iskanci

Talakawa su yasar da shashanci

Mui zaune cikin mutunci

Ba mai yi wa wani batanci

Majalisar dokokin Haurobiya dibge take da tsofaffin gwamna gwarangwam, tun daga zamanin Saurayin-kirinki kama ya zuwa yanzu da Lawallin Ahmadu ke jan ragama. Kuma daukacin ’yan makarantarmu da gama-garin Haurobiyawa na da masaniya kan irin ta’asar da aka tafka a kwanon tasar ta’asar majalisa tun daga zamanin Baba-ojo mai gonakin Ottawa, har zuwa kan Baban-burin-huriyya.

Babban abin dubi a madubin dubarudu a daukacin kadadar Arewatawa da Kudu, shi ne, ko wannan majalisar za ta ci gaba da tadiye Haurobiyawa su rasa inda mahukunta suka dosa. Sannan daidai wannan lokaci da ake ta tataburzar turka-turkar Fancon fincikar ficikar facaka, wai ’yn majalisarmu za su rika karbar rubin fanshon gwamna gwarangwam da daukacin wuraren da suka yi kwadagon laluben kadago, tun suna masu fuka-fukin tashi, har zuwa yanzu da tsufa ya cin musu?

Hakika Haurobiyawa sun koka da Wa-ka-ci-ka-tashin halin bera ba fashi, har ma da sukar mashi. Shi ya sa muke ganin in za ku tashi, ku tashi su ga fuskokinku ba murmushi. Sai a zo ai ta yi wa juna kallon ruduwa da duban hadarin kaji.

Kun ga shi ke nan, sai mu lallasa su su yi laushi, mu gasa su da garwashi; su ma su dandani kudarsu da haushi, har jikkunansu su yi yaushi. Shi ke nan an yi canjaras  ba bashi.

Daga nan sai a zo ai sasanci, inda  miyagu za su fasko cewa shayi ruwa ne, har su tuba da iskanci. Talakawa a yasar da shashanci

Mu yi zaune cikin mutunci, har ya zamto ba mai yi wa wani batanci, don ta haka ne kawai za a fita daga kunci.

Haurobiyawa, mu yi fafutikar hana fancon fincikar ficikar facaka, inda su gwamna gwarangwam da ke holewa a majalisar dokokin dukan ta-mola da talakawan kasar nan ke carafken cafke lada da la’adar daukacin kwadago da suka yi a kasar nan, na tsawon shekaru.

Lallai Lawallin Ahmadu ka yi wata doka ko garambawul ga wadda ake da ita, kan cewa masu mulkin mulaka’u su daina fancon fincikar ficikar facaka. Domin su ma ta wata sigar suna tatuke lalitar kasa, har su mayar da ita fanko, su yi wa talakawa fanco!

’Yan makaranta dai sanin kowa ne Dano mai alaye da gungun ’ya’yan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ba su da katabus din jirgawa, ballantana su jirkita kasar nan. Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo ku yi amfani da wannan damar, don ganin daukacin al’ummar kasar nan ana damawa da su, tun da yanzu ba sauran wanda zai damalmala musu al’amura. Tsintsiyar laushi da mai kwakwa a fara share wa al’umma jibgin jibar matsalolin da suka yi musu katutu, suke ta kawo wa kasa tarnaki.