✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fansho ga shugabanni: Yankin Birnin Abuja ya zama na farko a kananan hukumomin Najeriya

A yankin Birnin Tarayya Abuja da Minista ke mulki, babu tsarin dokar fansho ga tsoffin ministoci. Sai dai Karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC),…

A yankin Birnin Tarayya Abuja da Minista ke mulki, babu tsarin dokar fansho ga tsoffin ministoci. Sai dai Karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC), ta zama ta farko a tsakanin kananan hukumomi 774 na kasar nan, wajen kafa dokar ba tsofaffin shugabanni da mataimakansu da  shugaban majalisar kansilolin yankin da suke raye kudin fansho.

Sabuwar dokar wadda Shugaban Karamar Hukumar Malam Abdullahi Adamu Candido ya sanar lokacin zagayowar bikin samun ’yancin Najeriya karo na 59 a watan Oktoba da ya gabata. Ya ce duk tsohon Shugaban Karamar Hukumar da ba tsige shi aka yi ba, zai amfana da fanshon Naira dubu 500 duk shekara, sai Mataimaki dubu 300, sai Shugaban Majalisa Naira dubu 200.

Hakan na nufin duk shekara karamar hukumar za ta kashe Naira miliyan 6 kan rayayyun tsofaffin shugabanin karamar hukumar  6 da ke raye, da mataimakan shugabannin 6, sai kuma shugabannin majalisa 8.

Wannan mataki  ya sha suka daga kungiyoyin kare hakkin jama’a da  masu sharhi a kan al’amura, inda suka ce duk da cewa kudin bai da yawa idan aka yi la’akari da karfin karamar hukumar dokar za ta iya zama abin koyi ga sauran kananan hukumomin kasar nan, kuma adadin zai ci gaba da karuwa gwargwadon yawan shugabanni da za su mulki karamar hukumar.

Bayan kwanaki kalilan da sanarwar, wata kungiyar fafutika mai suna SERAP ta bai wa karamar hukumar mako biyu ta janye sabuwar dokar da ta ce ta saba  wa doka, ko kuma ta kai kararta kotu, sai dai Aminiya ba ta samu labarin abin da ya biyo bayan haka ba tun bayan sanarwar.