Categories: Manyan Gobe

Fara da tururuwa

Wata rana a lokacin bazara fara tana  zaune tana shan iska cikin kasala saboda irin koshin da ta yi kasancewar a wancan lokaci rayuwar tana da kyau da inganci. Tana nan zaune sai ta ji motsi a cikin ciyayi sai ta daga ganyayen da ke wurin domin ta ga abin da ke faruwa. Sai ta yi ido biyu da tururuwa sai ta ce mata me kike yi a nan haka? Sai Tururuwa ta ce “Kin gani masara nake tsinta don in kai rumbunmu saboda in yi tanadin gaba?

Sai fara ta kwashe da dariya ta ce ‘Don Allah zo mu yi wasa ko kya hutar da kanki daga wannan wahalar.”

ADVERTISEMENT

Sai tururuwa ta ce “Gaskiya ba zan iya ba, ina ganin ya kamata rumbunmu ya cika taf saboda lokacin sanyi, ke ma kuma ya kamata ki shirya.”

Sai fara ta kwashe da dariya ta ce “Ni ban damu da zuwan wani lokacin sanyi ba, bayan ga abinci nan baja-baja a ko’ina me zai dame ni?”.

ADVERTISEMENT

Ita dai tururuwa sai ta yi watsi da maganar fara ta ci gaba da jan masara tana kaiwa rumbunta. Ita kuma fara ta ci gaba da hawa kan ganyaye tana hutawa.

Ana nan sai yanayin sanyi ya zo, kuma ga shi an samu fari (karancin abinci).

Babu abinci ko’ina, duk abincin da aka noma ya kare. Nan fa hankalin fara ya yi matukar tashi saboda an wayi gari ba ta da ko kwayar da za ta sa a bakinta. Can sai ta tuna da tururuwa don haka ta nufi wurinta don ta taimaka mata da abin da za ta sa a bakin salati.

Mu kwana nan.

. .

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

12 hours ago