✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa za ta aike da tawagar ceto zuwa Lebanon

Shugaba Emmanuel Macron ya ce zai aike da ayarin ceto da magunguna Beirut bayana fashewar wani abu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa za ta tallafawa kasar Lebanon ta hanyar aikewa da ayarin ceto da magunguna bayan wata gagarumar fashewa ranar Talata.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya yi alkawarin aikewa da ayarin kwararrun jami’an ceto kimanin 55 hadi da wasu asibitocin tafi-da-gidanka zuwa birnin Beirut.

Macron ya ce ma’aikatan agajin da za su tashi daga birnin Paris nan ba da jimawa ba za su iya jinyar akalla mutum 500.

Kazalika, kasar za ta aike da kwararrun likitoci akalla 11 masu ayyukan gaggawa yayin da tuni rundunar Faransa dake aiki da ta Majalisar Dinkin Duniya dake kudancin kasar ta Lebanon tuni ta bi sahun masu aikin ceton.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya aike da ta’aziyyarsa kan mummunar fashewar da ta afka wa birnin na Beirut.

Mohammed ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba cewa, “Muna mika ta’aziyyarmu da juyayinmu ga al’ummar Lebanon, komai zai wuce”.

Ya ce Iran a shirye take ta ba Lebanon kowanne irin tallafi da take bukata.

A wani labarin kuma, kasar jamhuriyar Czech ma ta ce za ta aike da ayarin masu bayar da agaji zuwa kasar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Jan Hamacek ya ce wani ayarin ’yan kwana-kwana na musamman da ke da kwarewa wajen zakulo mutanen da gini ya danne za su bar kasar ranar Laraba.

Ayarin ya kunshi karnukan dake da ke da kwarewa wajen ceto, da kuma karin wasu mutane 30.

A ranar Talata ne dai wata mummunar fashewa a kusa da tashar jiragen ruwa ta kashe akalla mutane 100 tare da raunata akalla 4,000 a cewar kungiyar bayar da agaji ta Red Cross.