✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kayayyakin amfanin Gona ya fadi a yankin Saminaka

Sakamakon faduwar daminar bana, farashin kayayyakin amfanin gona ya fadi kasa warwas a yankin Saminaka da ya yi suna wajen noma a Najeriya. Wannan faduwar…

Sakamakon faduwar daminar bana, farashin kayayyakin amfanin gona ya fadi kasa warwas a yankin Saminaka da ya yi suna wajen noma a Najeriya.

Wannan faduwar da farashin kayayyakin amfanin gonar ya kara yi, ya sanya manoma da dama suna kokawa kan yadda zasu tunkari aikin noman wannan damina. Musamman ganin cewa da ma tun lokacin da aka girbe amfanin gonar kakar da ta gabata, farashin kayayyakin gonar bai yiwa manoma dadi ba.

Da yake zantawa da wakilinmu wani manomi kuma Sarkin babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka, Malam Isah Manu Idris, ya bayyana cewa gaskiya farashin kayayyakin amfanin gona a yanzu, musammana a wannan lokaci da ake shirye shiryen shiga  damina, bai yiwa manoma dadi ba. Domin kusan dukkan kayayyakin amfanin gona, farashinsu ya fadi kasa warwas.

Ya ce misali kamar  masara ada ana sayar da buhunta kan kudi naira dubu 8, zuwa dubu 8 da dari biyar zuwa dubu 9 amma yanzu, ana sayar da buhun masara naira dubu 6 wani lokaci ma har naira dubu 5 da dari 8.

Har’ila yau ya ce ada ana sayar da buhun wake soya naira dubu 17, amma yanzu ya dawo naira dubu 11.  A yayinda ada ake  sayar da buhun farin wake naira dubu 35, amma yanzu ya dawo naira dubu 13 zuwa naira dubu 14. Haka kuma ada ana sayar da buhun dawa naira dubu 9 amma yanzu ya dawo naira dubu 5 da dari 5 zuwa naira dubu 6.

Sarkin hatsin ya yi bayanin cewa wannan faduwar farashin kayayyakin amfanin gona shi ne ya sa manoma a halin yanzu, suke fargabar yin wani noman. Domin  wannan  al’amari ya kashe wa musu gwiwa.

Ya  ce babu shakka wannan faduwar farashin kayayyakin, zai kawo wa harkokin noma matsala a yankin Saminaka, a wannan damina. Domin manoma da dama suna ta barin gonakinsu, saboda ba su da kudaden da za su sayi taki, da biyan kudaden aikin gonakin.

Ya ce idan ka lura a baya manoma sun yi noma a wannan yanki, kuma  sun ci riba don haka kujerun aikin hajji a lokacin, kusan duk manoma ne suka biya.

‘’Muna ganin babban dalilin da yasa farashin kayayyakin amfanin gona ya fadi shi ne, mun ji labarin cewa gwamnati ta bayar da izini an shigo da kayayyakin amfanin gona daga kasashen waje,  musamman masara  an rabawa kamfanoni. Ya kamata gwamnati ta sayi wannan masara ta raba wa kamfanonin, maimakon sayowa daga waje. Wannan  ne zai sanya amfanin gonar ya yi daraja, ta yadda manoma za su sami karfin yin wani noman’’.

Sarkin hatsin ya ce babu shakka an yi kokari wajen  kafa kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona na Olan a Kaduna.

Ya ce ba dan wannan kamfani ba, da yanzu idan aka ce ana sayar da buhun masara naira dubu 3 da ba mamaki.

Ya yi kira  gwamnatocin jihohin Arewa su yi kokari su bude irin wadannan  kamfanoni na   sarrafa kayayyakin amfanin gona, a jihohinsu.