✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin man fetur ya karye

Saudiyya ta bayyana shirinta na kara yawan man fetur da take kaiwa kasuwar duniya yayin da farashin danyen man fetur ke kara karyewa a kasuwar.…

Saudiyya ta bayyana shirinta na kara yawan man fetur da take kaiwa kasuwar duniya yayin da farashin danyen man fetur ke kara karyewa a kasuwar.

Kamfanin man fetur na Saudiyya da ake kira Saudi Aramco ya bayyana kara yawan man fetur da kasar ke fitarwa zuwa kasashen ketare daga farkon watan Afrilu mai zuwa zuwa ganga miliyan 12.3 kowace rana, yayin da kamfanin ke kara fito-na-fito da kasar Rasha kan kudin man fetur a kasuwar duniya.

Mahukuntan Saudiyya sun fusata saboda Rasha ta yi watsi da shirin da kasashen masu arzikin man fetur na Kungiyar OPEC suka gabatar kan rage man fetur da ake kaiwa kasuwannin duniya da ganga miliyan 1.5. Maimakon haka Ministan Makamashi na Rasha, Aledander Nobak, ya bayyana shirin kara yawan man fetur da kasarsa ke kaiwa kasashen duniya daga ganga dubu 500 kowace rana zuwa ganga miliyan 1.7.

Wannan na zuwa ne yayin da farashin man fetur ya karye a kasuwannin duniya da kashi 25 cikin 100, inda farashin ya koma Dala 37 kan kowace gangar danyen man fetur.