✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesun dankalin turawa da kaza

Assalamu alaikum, uwargida a yau na kawo muku yadda ake girka farfesun dankalin turawa da kaza wanda aka fi sani a turance da ‘potatoe peper…

Assalamu alaikum, uwargida a yau na kawo muku yadda ake girka farfesun dankalin turawa da kaza wanda aka fi sani a turance da ‘potatoe peper soup’. Domin sanya kunnen maigida motsi, yakamata a rika dagewa wajen koyon girkin zamani. Girki dai shi ne sirrin zaman aure sannan iya girka abinci daban-daban na sanya maigida da yara cikin farin ciki da annashuwa inda za su rika rububin komawa gida da wuri.

 

Abubuwan da za a bukata:

· Kaza

· Dankalin turawa

·   Kori

·  ‘Thyme’

· Karas

·  Attarugu

·   Tumatir

·  Gishiri da magi

 

Hadi:

Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta yanka shi kanana, daga nan sai ka wanke zazanta. Ka fara tafasa kazar da attarugu da kori da garin tafarnuwa da citta nda magi da tumatir da ‘thyme’. Idan ya dan dahu, sai ki zuba yankakken dankalin turawar a ciki da koren wake da kuma yankakken karas.   Uwargida na iya yin irin wannan girki da safe don a karya.

Ina son janyo hankalin masu karatu cewa duk macen da take zuba man gyada a farfesu to da sauranta a girki, saboda farfesun kaza ko na kifi ko na nama da dai sauransu na dauke ne da kitsen ya wadatar.