✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesun kai da kafar rago

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda na kai da kafar rago. Kasancewar an gama…

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda na kai da kafar rago. Kasancewar an gama Sallah lafiya mata da dama an ajiye kai da kafar rago wadanda wadansu sai a ranar Cika-Ciki suke dafa su. Duk da yake akwai hanyoyi da dama da mata ke sarrafa nasu farfesun, hakan ya sanya na kawo muku irin namu salon dahuwar farfesun. In fada muku sirrin girki daya? Idan ana so a yi nasara a girki kowane iri ne, yana da kyau a yi amfani da kayan hadi kalilan domin idan suka yi yawa, musamman ma a farfe su, sai farfesun ya koma miya. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Kan rago da kafa da aka babbake
  • Attarugu
  • Albasa
  • Garin citta
  • Tafarnuwa
  • Maggi
  • Kori da thyme
  • Kayan kanshi
  • Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker)

Hadi

Bayan uwargida ta wanke ganda da tafasashen ruwa, sai ta dora ta bari ya sake tafasa domin cire maikon da ke jikin gandar. Za ta ga maiko ya yi sama sannan ta zubar da wannan ruwan sai ta kara  zuba wani ruwan a tukunyar dafa gandar domin sanyata ta nuna kuma ta yi laushi (idan ana wannan dahuwar a jira naman ya nuna ya yi laushi sosai kafin a zuba kayan hadi daga baya). Sai ta yayyanka albasa, ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa da citta kadan. Ta zuba magi da kori da thyme. Sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ta nuna na tsawon minti kadan sai ta sauke.

Ana son cin wannan girki da safe ko da dare. Wannan irin girki shi ne wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba illa a ci  don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wasu cututtuka. Da fata wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.