Da Dumi Dumi

‘Fasakwauri na gurgunta tattalin arziki’

Shugaban Hukumar Kwastam ta Qasa Kanar Hamid Ibrahim Ali
Shugaban Hukumar Kwastam ta Qasa Kanar Hamid Ibrahim Ali

Sabon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa, Shiyyar Kaduna, Alhaji Bashir Abubakar ya gana da manema labarai ciki har da Aminiya inda ya ce fasakwauri yana gurgunta tattalin arzikin kasa kuma ya ce hukumar tana kokarin tara wa kasar nan kudaden shiga:

Wane sako kake da shi ga al’ummar wannan shiyya?

Da farko ina mika sakon godiya ga al’ummar wannan yanki da ya hada da jihohin Kaduna da Katsina da Kano da Jigawa da Zamfara da Sakkwato da kuma Kebbi da Kogi da Kwara da Neja da Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wadannan su ne suke ke karkashin wannan shiyya tamu ta ‘Zone B’. Kamar yadda kowa ya sani aikin Kwastam aiki ne mai wuyar sha’ani sai dai dadinmu shi ne muna iya kokarinmu mu ga mun rage matsalolin jama’a.  Saboda wadansu na aikata laifuffukan ne a kan rashin sani domin sha’anin shiga da fita da kaya a kowace Kasa yana kawo ci gaban kasa kuma yana iya gurgunta tattalin arzikin kasa.

Zuwana wannan shiyya na fada wa ’yan uwana ma’aikata cewa za mu yi kokari mu bi lungu da sako domin ganawa da kungiyoyin ’yan kasuwa da shugabanni mu tunatar da su kan ayyukanmu wadanda dama sun sani suna da nasaba da dokokin kasa.

Abin da ka ga an hana shigowa da shi cikin  kasa ko aka bari a shigo da shi ba jami’an Kwastam ba ne suka hana ko bari a shigo da shi. Hasali ma lokacin da ake rubuta wadnnan dokoki babu jami’in Kwastam a wajen. Kamar aikin dan sanda ne an ce kada ka yi sata ko zalunci, lokacin da aka kafa wadancan dokoki babu dan sanda a wajen. Amma sai aka ce idan ka aikata dan sanda ya tuhume ka. To, haka aikinmu yake kan sha’anin shiga da fita da kaya . Idan ka ji an ce kada a shigo da mota, to, ba Kwastam ne ya hana ba, aikinsa shi ne kyautata tsaron kan iyaka don tabbatar da cewa ba a aikata abin da dokar kasa ta hana ba.

ADVERTISEMENT

Yaya batun tsaro a wannan yanki domin ka nuna cewa akwai damuwa?

Shi ya sa muka ce a shirye muke mu yi aiki da sauran jami’an tsaro da suke wannan yanki domin samun nasara. Sanin kowa ne a wannan shiyya tamu kashe-kashen jama’a ya yi yawa. Ana shigo da bindigogi da harsasai, musamman a jihohin Arewa maso Yamma, muna so mu ga wane hadin kai ne za mu samu daga wurin sauran jami’an tsaro masu yunifom da na farin kaya. Da kuma hadin kan da za mu samu daga shugabanin al’umma irin sarakuna da gwamnoni da ’yan majalisa yadda za mu samu mutanenmu su zauna lafiya. Wannan yana daga cikin abin da Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa Kanar Hamid Ibrahim Ali ya turamu mu yi.

Wane kokari kuke yi kan batun samar da kudaden shiga don inganta tattalin arzikin kasa?

Game da batun tattalin arzikin kasa za mu yi iyakacin kokarinmu domin abin da aka amince ka shigo da shi bayan ka biya haraji to ka tabbatar ka shigo da shi bisa ka’ida kuma ka biya wannan kudi ga gwamnati. Shi ya sa dokar Kwastam ta nuna cewa duk kudin da za ka biya na fito, ko na nuna ka kirkiro wani abu, to ka biya a banki da kanka kada ka bai wa wani ya je ya biya maka.  Sannan lambar asusun bankin da za a ba ka ka tabbatar na gwamnati ne ba na wani mutum ko kamfani ba. Saboda haka ina kira ga dukkan jama’ar  wadannan jihohi su ba mu goyon baya domin samun nasarar  habaka tattalin arzikin kasarmu.

Ko ana matsa muku wajen tara haraji ga kasa?

Kamar yadda ka sani ne aikinmu ne mu nema wa kasa haraji kuma abu ne da muka dade muna yi ana kuma samun nasara kuma za mu ci gaba da yin kokari domin ci gaba da samun nasara. Saboda idan zan amsa tambayarka zan ce babu wanda ke matsa mana domin tara haraji saboda Shugabanmu Kanar Hamid Ibrahim Ali da sauran shugabannin Kwastam sun amince da mu  kuma sun san muna aiki yadda ya kamata.

Shugaban namu, yanzu haka ya yi kusan shekara uku zuwa hudu a kan wannan mukami kuma bai taba bai wa Gwamnati kunya ba.  Kullum sai yabo da yake samu musamman a bangaren tara kudaden shiga.

Ana zargin a wasu lokuta a kan samu batagari a cikin ma’aikatanku da ke hada baki da masu fasakwauri suna shigo da kaya ta barauniyar hanya. Wane mataki za ku dauka domin magance matsalar?

Wannan zargi ne da mutane ke yi ba kuma mun ce babu irin wadannan jami’ai ba ne, amma idan har muka samu bayanai a kan masu irin wannan laifi kuma muka yi bincike aka tabbatar, dole a dauki mataki a kansu. Saboda haka muke kira ga ’yan jarida su tabbatar suna gudanar da bincike na kwarai idan aka ba su labari, mu kuma a shirye muke mu hukunta batagarin a cikin jami’anmu. Amma a yanzu haka jami’anmu na kokarin bin doka yadda ya kamata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya