✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar wasu abubuwa sun rushe gidaje a Akure

Fashewar wasu abubuwa ya firgita jama’a da yawa a hanyar garin Akure zuwa Owo da ke jihar Ondo da safiyar ranar Asabar. Fashewar abubuwan ya…

Fashewar wasu abubuwa ya firgita jama’a da yawa a hanyar garin Akure zuwa Owo da ke jihar Ondo da safiyar ranar Asabar.

Fashewar abubuwan ya yi sanadiyyar rushe daruruwan gidage da coci da makaranta, tare da raunata jama’a da dama da ke yankin kamar yadda wakilinmu ya tabbatar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Ondo Mista Adie Undie, ya tabbatar da aukuwar hakan, inda ya ce wasu abubuwan fashewa ne da wata mota ta dauko domin kai su muhallinsu zuwa jihar Edo sai motar ta samu matsala lokacin da take wucewa ta kan hanyar Akure zuwa Owo, kimanin kilomita biyu kafin filin jirgin saman Akure.”

Fashewar abubuwan ya faru ne da misalin karfe 1:00 na tsakar daren yau Asabar.

Jama’a da dama ne suka samu raunuka yayin fashewar.

Wasu gidaje da suka rushe Hoto daga shafin Twitter na Gwamnan jihar Ondo @RotimiAkeredolu