✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinjoji 41 suka mutu a wutar da ta kama jirgin sama a Moscow

Akalla fasinjoji 41 ne suka mutu bayan wani jirgin saman Rasha ya yi saukar gaggawa kuma ya kama da wuta a filin jirgin saman Sheremetyevo…

Akalla fasinjoji 41 ne suka mutu bayan wani jirgin saman Rasha ya yi saukar gaggawa kuma ya kama da wuta a filin jirgin saman Sheremetyevo da ke birnin Moscow.

Rahotanni da dama sun nuna fasinjoji na saukar gaggawa don kubuta daga cikin jirgin saman Aeroflot lokacin da ya tsaya yana cin wuta.

Kafofin yada labarai na Rasha da BBC sun ce akwai kananan yara biyu da wani ma’aikacin jirgi a cikin wadanda suka rasu.