✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 06

Babi na Biyu: Mai haila tana iya gyara gashin kan mijinta mai I’itikafi: 484. An karbo daga  Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba…

Babi na Biyu: Mai haila tana iya gyara gashin kan mijinta mai I’itikafi:

484. An karbo daga  Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Hisham ya ce, Babana ya ba ni labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) yana fitar mini da kansa lokacin da yake I’itikafi a Masallaci in gyara masa gashi, ta ce alhali ina haila.”

Babi na Uku: Mai I’itikafi ba ya shiga gida sai don wata bukata:

485. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labara daga dan Shihab daga Urwata da Amrat ’yar Abdurrahman cewa: “Lallai A’isha matar Annabi (SAW) – Allah Ya yarda da ita, ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana shigar mini da kansa alhali shi yana cikin Masallaci sai in tace masa. Kuma ya kasance ba ya shiga gida sai don bukata idan ya kasance mai I’itikafi.”

Babi na Hudu: Mai I’itikafi yana wanka:

486. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Mansur daga Ibrahim daga Aswad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) yana runguma ta ina haila. Kuma ya kasance yana fitar mini da kansa daga Masallaci yana I’itikafi sai in wanke masa ina haila.”

Babi na Biyar: I’itikafin dare daya:
487. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya dan Sa’id ya ba ni labari daga Ubaidiullahi ya ce, Nafi’u ya ba ni labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Umar ya tambayi Annabi (SAW) ya ce, “Na kasance a Jahiliyya na yi alwashi cewa, lallai zan yi I’itikafi dare daya a Masallacin Harami,” ya ce, “Ka cika alwashinka.”

Babi na Shida: I’itikafin mata:
488. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce, “Hammad dan Zaid ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba ni labari daga Amrata daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana I’itikafi a goma na karshen Ramadan. Kuma na kasance ina sanya masa mabuya (rumfa) yana shigarsa bayan ya yi Sallar Asuba. Sai Hafsatu ta nemi izinin A’isha ta kafa nata rumfar ta I’itikafi, sai ya yi mata izini aka kafa mata rumfa. Lokacin da Zainab ’yar Jahshi ta ga haka sai ta kafa wani rumfar. Lokacin da Annabi (SAW) ya wayigari sai ya ga wadannan rumfuna, sai ya ce, “Mene ne wannan? Sai aka ba shi labara. Annabi (SAW) ya ce: “Wannan da’a kuke nufi da su? Sai ya bar I’itikafin a wannan wata, sa’an nan ya yi I’itikafi a goma ga watan Shawwal.”

Babi na Bakwai: kananun rumfuna a cikin masallaci:

489. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Yahya dan Sa’id daga Amrata ’yar Abdurrahman daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi nufin yin I’itikafi lokacin da ya tafi zuwa ga inda yake nufin zaman I’itikafi, sai ya ga wasu lema (rumfuna), rumfar A’isha da rumfar Hafsa da rumfar Zainab sai ya ce, “Shin biyayya kuke nufi da yin wadannan? Sai ya juya bai yi I’itikafi ba har sai da ya yi I’itikafin a goma ga watan Shawwal.”