✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi Babi na Talatin da Tara:

Babi na Talatin da Tara: Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Ga wadanda ke da ikonsa (suna da zabin ko su yi azumi ko) kuma su…

Babi na Talatin da Tara:

Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Ga wadanda ke da ikonsa (suna da zabin ko su yi azumi ko) kuma su bayar da fansar abinci ga miskinai…(2:184).” dan Umar da Salmata dan Akwa’u sun ce: “Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.. ta shafe ta. Har zuwa fadarSa cewa: “Bisa ga abin Ya shiryar da ku tsammaninku kuna godewa. (2:184).” dan Numair ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, Amru dan Murrat ya ba mu labari ya ce, dan Abu Lailah ya ba mu labari ya ce, “Sahabban (Annabi) Muhammad (SAW) sun ba mu labari cewa: “Lokacin da ayar azumin Ramadan ta sauka sai haka ya yi tsanani a kansu, kuma sai ya kasance akwai wanda zai iya ciyar da miskini kowane yini ya bar yin azumi daga mai ikonsa (azumin). Sai aka yi musu rangwame a cikin haka, sai wata aya ta shafe ta da cewa: “Ku yi azumin shi ya fi muku alheri (2:184).” Sai aka umarce su da yin azumi gaba daya. (Fassarar wadannan ayoyi ya samu da ma’anoni daban-daban, wasu sun ce: Ayar ce ta shafe wata kamar yadda ya gabata,” wasu kuma suka ce, “A’a, ma’anar wadanda suke ikon yin azumi amma kuma tsufa ya hana musu, ko mace mai shayar da jariri, su ake nufin su biya fansa na ciyar da miskinai.” Don haka dan Umar ya yarda da ta farko, amma dan Abbas kuma ya yarda da ta biyu. Allah Ya sa mu dace).

409. An karbo daga Ghiyas ya ce: “Abdul A’alah ya ba mu labari ya ce, Ubaidullahi ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya karanata maganar: Ciyar da miskinai, sai ya ce, “An shafe ta.”

Babi na Arba’in:
Yaushe ya kamata a biya azumin Ramadan? dan Abbas ya ce, “Babu laifi a raba tsakaninsu, saboda fadar Allah Madaukaki cewa: “Biya na daga wasu kwanaki na daban.” Sa’id dan Musayyab ya ce, “Azumin goma ga Zul-Hajji ba ya yiwuwa sai mutum ya fara biyan Ramadan.” Ibrahim ya ce, “Idan mutum ya yi sakaci har Ramadan ya kewayo zai azumce su, amma bai ga hukuncin ciyarwa ba.” An ambata daga Abu Huraira bisa mursalin Hadisi haka daga dan Abbas cewa: Lallai shi (mai biyan) zai ciyar.” Amma dai Allah bai ambaci ciyarwa ba, abin sani dai Ya ce: “Biya na daga wasu kwanaki na daban.”:
410. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari daga Yahya daga Abu Salmata ya ce: “Na ji A’isha (Allah Ya yarda da ita), tana cewa: “Azumin Ramadan yakan kasance a kaina ban iya biya, face sai watan Sha’aban.” Yahya ya ce, ta ce: “Saboda ayyukan Annabi (SAW).”

Babi na Arba’in da daya:
Mai haila tana barin azumi da Sallah. Abu Zinad ya ce, “Lallai sunnoni da gaskiya bayyananu suna zuwa su tsare ra’ayoyi, wanda babu makawa ga mutum Musulmi ya bi su. Daga irinsu akwai maganar cewa: Mai haila tana biyan azumi, amma ba ta biyan Sallah.”
411. An karbo daga dan Abu Marya ya ce: “Muhammad dan Ja’afar ya ba mu labari ya ce, Zaid ya ba ni labari daga Iyad daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Ashe idan mace ta yi haila ai ba ta Sallah? To wannan shi ne nakasar addininta.”