✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fataken da ke taimaka wa barayin shanun Zamfara sun shiga hannu a Legas

’Yan sanda sun kama wadansu fataken shanu a Kasuwar Dabbobi ta Abatuwa da ke Agege, Legas da ake zargi da taimaka wa masu yin garkuwa…

’Yan sanda sun kama wadansu fataken shanu a Kasuwar Dabbobi ta Abatuwa da ke Agege, Legas da ake zargi da taimaka wa masu yin garkuwa da mutane tare da satar shanu a Jihar Zamfara.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta bayyana ’yan kasuwar shanun da ake zargi masu suna Alhaji Ago Altine da Alawani Abubakar da Mohammed Shagari da Bashiru Aliyu

Masu sayar da shanun sun shiga komar ’yan sandan ne bayan da rundunar ta yi nasarar kama daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ’yan matan nan ’yan biyu a Jihar Zamfara mai suna Nafi’u Usman wanda shi ne ya bayyana cewa gungun barayin shanun suna samun kudin sayen makamai ne ta hanyar haramtaccen kasuwancin shanu da suke yi da wani falke mai suna Alhaji Naira wanda shi su ke bai wa shanun yana zuwa da su kasuwar shanu ta Legas yana raba wa wadanda ake zargin, inda bayan sun sayar su aika masa da kudin wadanda da su ne suke sayen bindigogi daga kasar Libiya.

Nafi’u Usman wanda ya ce Naira dubu 500 aka ba shi a cikin Naira miliyan 15 da aka biya kudin fansar garkuwa da tagwayen ’yan matan na  Zamfara, shi ne ya bai wa ’yan sandan bayanan Alhaji Naira wato falken da yake musu safarar shanu zuwa Legas bayan da  ’yan sandan sun kama shi ne ya bayyana mutum hudun da ke sayar musu da shanun.

Daya daga cikin wadanda ake zargi mai shekara 50 mai suna Altine ya ce ya sayi saniya sama da 400 daga falken. Amma ya ce ba ya da masaniyar cewa shanun na sata ne. Ya ce yakan sayi saniya guda a kan Naira dubu 60 ko 70 inda shi kuma yake sayarwa Naira dubu 170 zuwa 180, ya ce yana tura kudin a asusun ajiyar Alhaji Naira ne amma ba ya da masaniyar abin da yake yi da kudin.