Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Fati Washa ta samu mabiya miliyan 1 a shafin Instagram

Fitacciyar jarumar ‘yar wasan fina-finan Hausan nan, Fati Washa, ta yi nasarar samun mabiya miliyan daya a shafinta na Instagram.

Jarumar ta sami damar hakan ne bayan ta wallafa sau 710 kacal a shafin nata na sada zumuntar Instagram.

ADVERTISEMENT

Domin nuna murnar wannan cigaban, jarumar wacce ke bibiyar/biyar mutane 580 kacal a shafin Instagram dinta, ta dangana da shafin nata na Instagram wajen nuna farin ciki tare da godiyarta.

Fati Washa, ta wallafa a shafin nata cewa: “Ina matukar godiya gare ku, masoyana, tare da dukkan wanda ya taimaka wajen cimma hakan. Na gode mu ku, kuma ina kaunar ku. Ban taba tunanin cewa zan sami mabiya har miliyan guda, Ramadan Kareem”.

ADVERTISEMENT