✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fatima Mamman Daura ce ta dauki bidiyo na ina fada, Cewar Aisha Buhari

Baraka ta kunno kai a Fadar Shugaban Najeriya a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa, Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matarsa Aisha kishiya.…

Baraka ta kunno kai a Fadar Shugaban Najeriya a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa, Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matarsa Aisha kishiya.

A kwanakin nan aka yi ta yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda a cikinsa aka ga wata a cikin daki ba tare da nuna fuskar mai magana ko daukan hoto ba, wanda aka ce muryar uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ce tana ta fada da harshen turanci tana gaurayawa da Hausa, tana cewa “Ina daya daga cikin dakin da yake da cikkaken tsaro inda akalla akwai sama da ‘yan sanda 200 da sojoji 200 da ke tsaron mu, akan me za a rufe min daki?”.

BBC ta samu jin ta bakin Aisha Buhari, inda ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

Ta kuma yi karin haske cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta nadi bidiyon da ake tafka mahawara shafukan sada zumunta a kai.

Sai dai ko da BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta musanta daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

A cikin bayanin da Aisha Buhari ta yi a harshen turanci, bayan saukar ta a filin jirgi a Abuja ta bayyanawa manema labarai cewa lallai ita ce a wannan bidiyo kuma lamarin ya faru ne a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Aisha, ta ce: “Jami’an tsaro na suna wurin amma sun kasa yin komai domin ‘yar gidan Mamman-Daura Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin.”

Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi ma ta dariya kuma ita ce ta rufe ma ta kofar dakin ajiyar kayayyaki.

Rahoton BBC Hausa