✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FC Barcelona ta yi sabon koci

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya bayar da sanarwar nada sabon koci mai suna Gerardo Tata…

Sabon Kocin FC Barcelona Gerardo Tata MartinoA ranar Talatar da ta wuce ne kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya bayar da sanarwar nada sabon koci mai suna Gerardo Tata Martino a kwantaragin shekara uku.
Sabon koci Gerardo ya maye gurbin tsohon kocin kulob din ne mai suna Tito bilanoba bayan ya ajiye aiki a ranar Juma’ar da ta gabata saboda ciwon dajin da ke damunsa.
Tsohon kocin ya bayyana sanarwar ajiye aikinsa ne a lokacin da ya lura ba zai iya cigaba da harkar koyarwa a kulob din ba musamman ganin ba shi da koshin lafiya.
Jaridar Marca da ake wallafata a Sifen ta ruwaito cewa sabon koci Gerardo wanda ya taba horarwa a kulob din Newell’s Old Boys da ke Ajantina ana sa ran zai kama aiki a kulob din Barca ne tare da masu taimaka masa watau Elbio Paolorroso da Jorge Pautasso.
dan kwallon Ajantina da FC Barcelona, Lionel Messi yana daya daga cikin magoya bayan sabon kocin. A cikin hira da jaridar Portal Ole da ke Ajantina ta yi da shi a shekarar 2012 ya bayyana kocin a matsayin daya daga cikin wadanda yake kauna.