✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ferguson zai hada kai da Solskjaer wajen horar da Man United

Kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada tsohon kocin kulob din Sa Aled Ferguson a matsayin wanda zai hada kai…

Kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada tsohon kocin kulob din Sa Aled Ferguson a matsayin wanda zai hada kai da sabon koci Ole Gunnar Solskjaer don ci gaba da horar da ’yan wasan kulob din.

A ranar Talata ce kulob din ya ba da sanarwar dauka wannan mataki don Ferguson ya taimaki sabon kocin da basirar da Allah Ya hore masa don ganin an kai ga samun nasara, kamar yadda jaridar Sun Sport ta Ingila ta kalato.

Solskjaer yana daga cikin ’yan kwallon da Sa Aled Ferguson ya taba horarwa. Kuma yana daga cikin ’yan wasan da suka taba lashe wa United manyan kofuna a 1999.  Kofunan sun hada da gasar Firimiya ta Ingila da Kofin Zakarun Turai da Kofin Kalubale na Ingila (FA).  Tun daga wancan lokaci kawo yanzu United ba ta sake samun irin wannan nasara ba.

Rahotannin sun ce Solsjaer ne ya bukaci mahukunta kulob din su dawo da Ferguson don su ci gaba da aiki tare don hakan zai daukaka martabar kulob din.

Ole Gunnar Solsjaer zai ci gaba da horar da United ne har zuwa karshen kakar wasa ta bana bayan da kulob din ya sallami Jose Mourinho a matsayin koci a makon jiya.

Da yawa daga cikin magoya bayan United sun nuna farin ciki game da wannan mataki da kulob din ya dauka na sake dawo da Sa Aled Ferguson a matsayin mai horarwa.