✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta fitar da kudin tikitin shiga gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil

Hukumar kula da shirya kwallo ta duniya (FIFA) a shekaranjiya Laraba ne ta fitar da kudin shiga gasar cin kofin duniya da zai gudana a…

Mista Sepp Blatter Shugaban Hukumar FIFAHukumar kula da shirya kwallo ta duniya (FIFA) a shekaranjiya Laraba ne ta fitar da kudin shiga gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Mafi karancin kudin tikitin shiga filin wasa da ’yan kasar za su  shi ne na  Dala 15 kwatankwacin Fam 10 inda ya yi daidai da Naira dubu 2 da 600.  Wannan kuma zai kasance ne ga dalibai da kuma tsofaffin da suka haura shekara 60.  Sannan mafi yawan kudin tikiti ga mazauna kasar za su sayin tikiti a yayin gasar shi ne na Dala 90 ko Fam 59 kwatankwacin Naira dubu 15.
Ga mazauna ketare kuwa, mafi karancin tikiti shi ne na Dala 440 ko Fam 288 kwatankwacin Naira dubu 75 yayin da mafi tsada kuma shi ne na 990 ko Fam 650 kwatankwacin Naira Naira dubu 169.
Hukumar ta kara da cewa, a ranar 20 ga watan Agustan wannan shekara ce ake sa ran za a fara sayar da tikitin.
Wannan kudin tikiti da hukumar ta fitar ya yi daidai da wanda ta sayar a lokacin gasar cin kofin duniya da ya gudana a Afirka ta Kudu a shekarar 2010 inda farashin ya kama daga Fam 14 zuwa Fam 630.
Sai dai zanga-zangar da ta gudana a kasar Brazil a lokacin gasar cin kofin Nahiyoyi (Confederations Cup) ta sa shugaban Hukumar FIFA Mista Sepp Blatter ya fara tunanin ko hukumar ta yi zaben tumun-dare wajen daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa.

… Yayin da ta dage dakatarwar da ta yi wa Kamaru

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta dage dakatarwar da ta yi wa kasar Kamaru daga shiga harkar kwallo.
Tun a farkon watan Yulin da muke ciki ne dai hukumar ta kage kasar daga shiga dukkan harkokin wasannin da ta shirya saboda abin da ta kira yin katsalandan da gwamnatin kasar ke yi  a Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Kamaru.
Hukumar ta ce saboda yadda kasar ta yi nadama kuma ta koma kan bin ka’idojin da hukumar ta shimfida ne ta sa Hukumar janye dakatarwar.
Don haka a yanzu kasar za ta cigaba da fafatawa a dukkan wasannin da Hukumar ta shirya a ciki da kuma wajen kasar.
“Da wannan dagewar, kungiyoyin kwallon kafa da ke kasar da jami’ansu za su cigaba da shiga harkokin wasan kwallo ba tare da wani cikas ba”, kamar yadda sanarwar da Hukumar ta fitar a yanar gizonta ya nuna.
Ana sa ran a ranar 3 ga watan Satumban wannan shekara da muke ciki ne Kamaru za ta fafata a wasan karshe na neman hayewa zuwa gasar cin kofin duniya da Libya.
Kamaru dai tana daya daga cikin manyan kasashen Afirka da ake ji da su a harkar kwallo.  Ta halarci gasar cin kofin duniya sau shida kuma ta taba lashe gasar cin kofin Afirka sau hudu.