Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

FIFA ta zabi ’yan kwallo 10 da za su fafata a Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya na bana

A shekaranjiya Laraba ce Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta zabi ’yan kwallo 10 da za su fafata a Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya ta Bana.

Daga cikin ’yan kwallon da aka zabo akwai Cristiano Ronaldo dan kwallon Jubentus da ke Italiya da Lionel Messi dan kwallon FC Barcelona na Sifen da Mohammed Salah da Sadio Mane ’yan kwallon Liberpool da ke Ingila da sauransu.

ADVERTISEMENT

Sai dai abin mamaki shi ne babu dan kwallo ko daya daga kulob din Manchester City na Ingila duk da lashe kofuna uku da kulob din ya yi a bana.

Sannan dan kwallon Real Madrid Luka Modric, wanda ya lashe gasar a bara kuma ya taka wa Ronaldo da Messi birki bayan sun shafe shekara 10 suna lashe kyautar a tsakaninsu, ba ya cikin wadanda za su fafata a bana.

ADVERTISEMENT

Ana sa ran hukumar za ta sanar da dan kwallon da ya lashe gasar ta bana ce a ranar 23 ga watan Satumban bana a birnin Milan na kasar Italiya.

Ronaldo da Messi ne suka fi yawan lashe wannan kyauta inda kowannensu ya lashe sau biyar-biyar.