✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filato ta kasafta Naira biliyan 172  a badi

Gwamnatin Jihar Filato ta kiyasta kashe Naira biliyan 172 da miliyan 596 da dubu 317 da 577 a kasafin kudinta na badi. Gwamnan Jihar Simon…

Gwamnatin Jihar Filato ta kiyasta kashe Naira biliyan 172 da miliyan 596 da dubu 317 da 577 a kasafin kudinta na badi.

Gwamnan Jihar Simon Lalong ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da kasafin kudin a gaban Majalisar Dokokin Jihar Filato.

Gwamna Simon Lalong ya ce kasafin kudin ya haura na bana da Naira biliyan  19 da miliyan 59 da dubu 127 da 508.

Ya ce kasafin kudi na badi an ware Naira biliyan 98 da miliyan 146 da dubu 697 da 900, wato kashi 56.86 don gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware Naira biliyan 74 da miliyan 449 da dubu 619,da 677 wato kashi 43.14 na kasafin kudin don gudanar da ayyukan raya kasa.

Ya ce an ware wa bangaren mulki Naira biliyan 11 da miliyan 681 da dubu 25, sai banaren ilimi Naira biliyan 10 da miliyan 744 da dubu 674 da 677.

Haka zalika ya ce an ware wa harkokin samar da ruwan sha Naira biliyan 15 da miliyan 574 da dubu 850, sai Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri  Naira biliyan 14, da miliyan 30.

Kasafin ya nuna cewa za a kammala hanyoyi  28  da wannan gwamnati ta gada, daga gwamnatocin da suka gabata tare da kammala hanyoyi da gadoji 25 da gwamnatin ta fara.

An ware wa Ma’aikatar Lafiya Naira biliyan 4 da miliyan 566 da dubu 500 don gyara asibitoci da gina sababbi a garuruwa, daban-daban na jihar.