Da Dumi Dumi

Filato United ta yi wa jaridar Aminiya ta’aziyyar rasuwar Bashir Liman

A ranar Litinin da ta wuce ce mahukuntar kulob din Filato United da ke Jos suka aiko da sakon ta’aziyya ga Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya kan rasuwar wakilin Aminiya  a Jos, Bashir Musa Liman.

A sakon da Kakakin Kulob din Albert Dakup ya sanya wa hannu ya ce “kulob din Filato United ya girgiza da samun labarin rasuwar Bashir Musa Liman, na jaridar Daily Trust da Aminiya.  Ya ce babu shakka kulob din ya rasa zakakurin dan jarida da yake taimaka wa kulob din Filato United wajen yada manufofinsa ga daukacin duniya.  “Bashir Liman, dan jarida ne da ya san aikinsa, kuma yake tare da kulob din Filato United a lokaci mai tsawo don haka kulob din ba zai taba mance irin gudunmawar da ya bayar wajen daukaka martabar kulob dinmu ba,” inji shi.

Shi ma Janar Manajan kulob din Pius Henwan ya bayyana alhininsa game da rasuwar Bashir Liman.  Ya bayyana shi a matsayin dan jaridar da ke yada manufofin kulob din tun a shekarar 2016 da kulob din ya sake komawa Rukunin Firimiya.

Bashir Liman, dan shekara 34 ya rasu ne a ranar Asabar da ta wuce a wani hadarin mota da  ya rutsa da shi a Ningi da ke Jihar Bauchi.  Ya rasu ya bar iyaye da ’yan uwa.

 

ADVERTISEMENT

 

Share