✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firayi Ministar New Zealand ta jawo Hadisin Manzon Allah domin jajanta wa Musulmin kasar

Firayi Ministar New Zealand Jacinda Ardern ta jawo wani Hadisin Manzon Allah (SAW), lokacin taron addu’o’in tunawa da Musulmin da  wani dan ta’adda ya kashe…

Firayi Ministar New Zealand Jacinda Ardern ta jawo wani Hadisin Manzon Allah (SAW), lokacin taron addu’o’in tunawa da Musulmin da  wani dan ta’adda ya kashe a masallatai biyu ranar Juma’ar makon shekaranjiya.

Ta jawo wani Hadisin da aka ruwaito Annabi Muhammad (SAW) yana cewa “Wadanda suka yi imani, masu kyautata wa juna ne da tausayi da jinkai, kuma suna nan kamar jiki daya ne. Idan daya daga cikin gabar jikin ta yi ciwo, to sauran jikin ma yana jin zafin ciwon.”

Firayi Ministar ta kara da cewa, “Kasar New Zealand tana alhini tare da ku, mu da ku abu guda ne.” kamar yadda BBC ya ruwaito a wani faifan bidiyo.

Har ila yau, kafafen watsa labarai a kasar sun sanya kiran Sallah da kuma yin shiru na minti biyu don martaba Musulmin da aka kashe a harin masallacin na Al-Noor a birnin Christchurch.

Firayi Ministar ta je wurin da dubban masu makoki suka taru a kusa da masallacin, wato daya daga cikin wuraren da wani mahari ya bude wa Musulmi wuta tana sanye da lullubi a kanta.

Imam Gamal Fouda, wanda ya jagoranci sallar ya ce: “Muna cikin bakin ciki, amma hakan bai sa mun karaya ba.”

Kusan mutum 50 dan bindigar ya kashe, wadansu kuma da dama suka ji raunuka kamar yadda Aminiya ta ruwaito a makon jiya.