✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firayiministan Latbia ya yi murabus saboda rufin kwano ya kashe mutum 54

Firayiministan Latbia ya yi murabus saboda rufin kwanon wani katafaren kantin sayar da kayayyakin masarufi, inda mutum 54 suka mutu.Wannan mataki da Firayiminista baldis Dombrobskis’…

Firayiministan Latbia ya yi murabus saboda rufin kwanon wani katafaren kantin sayar da kayayyakin masarufi, inda mutum 54 suka mutu.
Wannan mataki da Firayiminista baldis Dombrobskis’ ya dauka zai kawo wa jam’iyyarsa ta nakasu, kodayake shi ne Firayiministan da ya fi kowane dadewa a karagar mulkin tun bayan da kasar ta samu ’yancin kanta daga kasar Rasha.
“Bisa la’akari da wannan mummunan hadari, tare da sauran al’amuran da suka auku, wannan kasar na bukatar gwamantin da ke da dimbin goyon baya a majalisa, ta yadda za ta iya warware matsalolin da ka iya taso wa kasa,” a cewar Dombrobskis,  jawabin da ya yi wa manema labarai, bayan ya yi wata ganawa da Shugaban kasar, Andris Berzins.
A makon da ya wuce ne, wani katafaren kantin sayar da kayyakin masarufi na ‘Madima Supermarket’ rufinsa ya fado, ind aya halaka mutum 54, kuma wannan ita ce musifa mafi muni da ta auka wa kasar, tun bayan da ta samu ’yancin kai daga kasar Rasha a shekarar 1991. Tuni ’yan sanda suka fara gudanar da bincike kan musababbin fadowar rufin kwanon.
Daga cikin dalilan daka yi hasashen sun haddasa rushewar gini, sun hadada zayyana mara kyau da amfani da kayan gini marasa nagarta, tare da cin hanci da rashawa.Rufin kwanon da ya kashe mutum 54 a kasat LatbiaDombrobsky ya kama ragamar mulki ne tun a shekarar 2009, a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ya fara durkushewa. Tuni dai Shugaba Berzins ya fara laluben wanda zai maye gurbin tsohon Firayiministan. Daga cikin nasarorin da ya samu sun hada da farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya fara yin kafada-da-kafada da sauran kasashen Tarayyar Turai. Kuma a ranar 1 ga janairun badi ake sa rana Latbia za ta shiga cikin jerin kasashen Tarayyar Turai, inda za ta rika amfani da kurin Euro.