✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiya ta Ingila: Gobe za a shawo ta tsakanin Liberpool da Arsenal

A gobe Asabar ce ake sa ran za a fafata wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da na Arsenal a gasar Firimiya ta Ingila.…

A gobe Asabar ce ake sa ran za a fafata wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da na Arsenal a gasar Firimiya ta Ingila.

Wannan shi ne wasan farko a zagaye na biyu, bayan da aka kammala wasan zagaye na farko a shekaranjiya Laraba.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake saman teburi, yayin da kulob din Arsenal kuma yake matsayi na 5.

Tun daga wasan na gobe kungiyoyin kwallon kafa da ke gasar za su fara sanin makomarsu ganin yadda gasar ta fara zafi.

Ana sa ran a makon gobe ne za a bude kasuwar cinikin ’yan kwallo inda kulob da dama suka shirya cefano ’yan kwallo don karfafa kungiyoyinsu.

Kawo yanzu kulob din Liberpool dai bai samu rashin nasara a gasar ba yayin da Arsenal ta samu rashin nasara sau uku.

Kungiyoyin da ke sahun farko sun hada da Liberpool a matsayi ta farko sai Manchester City a matsayin ta biyu, sai Tottenham a matsayi ta 3 sai Chelsea a matsayin ta hudu sai Arsenal a matsayi ta biyar sai Manchester United a matsayi ta shida.

Kungiyoyin da suke kasar teburi sun hada da na Fulham da Huddersfield Town da kuma  Burnley.