✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitar dodon Oloolu ta sa rufe kasuwanni a Ibadan

Yau fiye da shekaru 300 ake gudanar da wata al’adar gargajiya ta bikin fitowar dodanni da mabiyansu da ke zagaya sassa daban-daban na birnin Ibadan…

Yau fiye da shekaru 300 ake gudanar da wata al’adar gargajiya ta bikin fitowar dodanni da mabiyansu da ke zagaya sassa daban-daban na birnin Ibadan a kowace shekara. Idan sun fito sukan fara kai ziyarar gaisuwar ban girma ga Mai martaba Olubadan na Ibadan ne domin samun umarnin fitar tasu. Akwai wasu fitattun hakimai a cikin jerin manyan mutanen da suke karbar bakuncin dodannin a gidajensu. Gwamnan Jihar Oyo, yana daga cikin manyan mutanen da ake kai wa gaisuwar ban girma a ofishinsa. Dodannin, suna yin kwanaki 14 cif suna wannan biki.
Tarihi ya nuna dodon Oloolu, wanda yake babba a cikin dodannin, bayan fitowarsa babu wani dodo da zai sake fita sai wata shekarar, an ce mata sukan mutu idan sun yi ido hudu da shi. Yakan yi kwanaki uku yana zagaya gari ba tare da yin ido hudu da kowace irin mace ba.
Wannan ya  sa mata ’yan kasuwa sun rufe rumfuna da kantuna da shaguna a kan hanyoyin birnin Ibadan, wadanda ayarin dodo Oloolu ya ke ziyarta, suna boyewa cikin gidaje har zuwa wucewar dodon, sai su koma ga harkokin kasuwancinsu, domin wasu hanyoyi daban dodon yake bi wajen komawa gida.
Ranar Talata ne dodon ya fita tare da dimbin mabiyansa a birnin Ibadan. Wakilinmu, ya je gidan dodon,  wanda ke unguwar Ode-Aje Aremo, ya ga irin al’adun da ake gudanarwa. Cikin abin da dodon ke rikewa har da wani kokon kan mutum. An ce kokon kan na ‘yar Oloolu na farko ne, wanda ya yi kicibis da ita lokacin da yake komawa gida, nan take ya ce “Dara ta ci gida,” ya shanye jininta ta mutu. Tun daga wancan lokaci ne sauran dodanni na Oloolu da suke fita a kowace shekara suke amfani da wannan kokon kai domin tabbatar da gaskiyar cewa, mata ba sa yin ido hudu da Oloolu, idan kuwa suka ga juna to, mutuwa za su yi.
 Jama’a, musamman ’yan siyasa da suke amfani da wannan dama ta fitowar dodannin su cusguna wa masu hamayya da su, ba su samu yadda suke so ba, domin tun ranar Litinin Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammed Abdlkadir Indabawa, ya tsara jami’an tsaro, ’yan sanda da sojoji da za su bi jerin gwanon Oloolu da mabiyansa zuwa wuraren ziyarar tasu domin guje wa tashin hankali.
Makonni biyu baya, wani dodo da mabiyansa sun shiga gidan wani shugaban kungiyar direbobi a Ibadan suka yi masa kisan gilla. Duk da yake ’yan sanda sun kama wasu na kusa da wancan dodo da ya tsere, kwamishinan ya ce, “a wannan karo, mun yi kyakkyawan shirin ko-ta-kwana domin ganin dodon Oloolu da mabiyansa sun yi bikinsu lafiya, ba tare da cin zarafin mutanen gari ba.” A ranar Talata kuwa tun da sassafe aka girke jami’an tsaron don tabbatar da haka.
 Kafin dodo Oloolu ya fito, sai da jama’arsa suka bayar da sanarwa ga mata su kulle kawunansu a cikin gidajensu. Dodon ya fito ne sanye da wata riga da wando da hula mai launin shudi da aka dinke su a hade yana rike da kokon kan mutum a hannun hagunsa da wata bulala a hannun dama da wani gajeren asawaki da yake taunawa, tare da wani karamin mutum-mutumi da aka sassaka da wasu murjanai a wuyansa. Daga nan sai ya doshi wasu dakunan tsafi guda biyu da ke dab da gidan, ya yi wasu maganganu da aka ce addu’ar neman sa’ar fita da dawowa ce. Akwai wasu bakaken duwatsun marmara kamar guda takwas da aka girke su a gindin wata bishiya da yankakken kan kare a kansu da aka barbada musu manja, su ma sai da ya yi wasu maganganu a kansu, kafin ya fice zuwa fada. Duk a wannan lokaci bai lullube fuskarsa da hular da ke manne da rigar da yake sanye da ita ba. Daga nan sai makadansa na musamman suka fara irin kidinsu, aka kama hanya zuwa fadar Olubadan, wadda ke Aremo, a kusa da gidan wannan dodo, domin kai gaisuwar ban girma. Dodon tare da mukarrabansa  wadanda su ma suke sanye da tufafi irin na mayaka da tsumangi a hannayensu suna yin tafiyar sassarfa ne. A wani lokaci sai ya juyo baya, yana neman wanda zai shabda wa bulala, amma sai a dare a bar shi, sai kuma ya juya, ya ci gaba da tafiya.
A yayin da suka isa fada, shi kadai da manyan mabiyansa kamar su 10 kawai aka kyale su shiga, inda suka fara raye-raye da kirari da wakar tabbatar Oloolu ya iso ga sarki. Bayan kammala kidan ne sai Oloolu, ya shaida wa Olubadan na Ibadan Oba Samuel Odulana Odugade cewa ya fito neman iznin fitar ne tare da yin addu’a ga sarki. Ekarun Olubadan, Cif Edward Oyewole Foko, shi ne ya wakilci Olubadan, nan take ya nuna amincewar fitowar tare da mika wa dodon kyautar kudi a cikin ambulan da kwalaben giya masu tsada a matsayin kyautar Olubadan. Mukarraban dodon Oloolu, sun ja kunnen wakilinmu da kada ya kuskura ya dauki hoton dodo ko nadar muryarsa.
Ekarun Olubadan, Cif Edward Oyewole Foko, wanda shi ne na biyar daga cikin jerin masu jiran gadon Olubadan, ya tuntuba wa wakilinmu kadan daga tarihin dodon. Ya ce, “Al’adar Oloolu ta shekara 300, a zamanin Ibadan ta farko da al’amarin ya sukurkuce ya haifar da rabuwar al’umma a dalilin irin wannan biki saboda dodon yana shiga cikin kasuwanni yana taka rawa ba tare da sanya irin tufafin da aka yarda cewa, ba mutum ba ne shi. A dalilin haka ne tsafin nasu, a wancan lokaci, ya bayar da umarnin a rusa dukkan garin da irin wannan al’amari ya auku a cikinsa. A shekara ta 1829 da birnin Ibadan ya sake bayyana a karo na biyu, aka dawo da kyautata wannan al’ada har zuwa yanzu da dodon yake bayyana a kowace shekara domin girmama al’adun namu.”
Wani Bahaushe masanin tarihin Yarabawa da aka haife shi a birnin Ibadan, mai suna Sarkin Ruwan Ibadan, Alhaji Bala Ibrahim ya bayyana wa Aminiya cewa, “Dodon Oloolu, babba ne a cikin dodanni, wanda ya samo asali daga tsafin Oro, wanda ke nufin duk abun da mata ba sa ganinsa. Har yanzu sauran garuruwan Yarabawa suna amfani da shi, amma a Ibadan, sai aka sauya masa suna zuwa Oloolu. Sarakuna suna karrama shi kuma mata suna iya ganinsa, amma shi ba zai yi ido hudu da su ba. diyar Oloolu na farko ta mutu ne a dalilin yin kicibis da ita bayan dawowarsa daga yawo wanda ya shanye jininta  kuma aka yanke kokon kanta ake amfani da shi yanzu domin tsoratar da jama’a, musamman mata, domin su amince cewa, ga shi ya fara daga gidansa. A zamanin jahiliyya ana yin amfani da shi ne idan za a tafi yaki ko an dawo ba a yi nasara ba; ko hangen bullar wata annoba, sai a nemi shawararsa domin sanin inda aka nufa. Ma’anar Oloolu, shi ne ‘mabugi’ da masu rinin suturu suke amfani da shi. Idan ya fito kuma zai yi kwanaki 3 yana yawo dare da rana ne sannan a karshe ya koma gida a rana ta 3.”
Alhaji Bala Ibrahim, wanda yanzu haka yana daga cikin kansilolin karamar hukumar riko ta Akinyele a Jihar Oyo, ya ce, “Ainihin dodannin Oloolu da suka shude ba sa rike bulala ko tsumangiya, yanzu ne aka fito da wani sabon salo na zamani da suke yawo da makamai, saboda wasu ’yan siyasa suna amfani da su a matsayin ’yan banga da suke tayar da hankulan jama’a. Kuma, a wancan lokaci, ba za ka iya kusantar dodon ba, a dalilin irin doyi da ke fita daga jikinsa, saboda jinin dabbobi da na mutane da aka yayyafa masa da wasu tsubbace-tsubbace.”
Dangane da mutuwar matar da Oloolu ya ganta, Sarkin Ruwa Bala ya ce lamarin ya danganta da imanin mace ne. “A yanzu komai ya canza, domin ko ya gansu babu abun da yake faruwa. A shekarar 1976 Sheikh Abdul Azeez Ajagbemokefiri ya fito da matansa 4 da ’ya’yansa mata da wasu mata musulmi daban ya tunkari dodon Oloolu da ya fito ya gaya masa karshen bayyanarsa ta zo. Ya kwace kokon kan da sauran kayan tsubbun da ke hannun dodon, ya keta rigar da yake sanye da ita, ya yi masa dukan tsiya, ya fatattake shi, kuma babu abun da ya faru ga matan. Mabiyan dodon  sun shigar da kara kotu, suka yi nasara a dalilin dokar kasa da ta amince wa kowa yin addinin da yake so. Shi ne dalilin ci gaba da bayyanar wannan dodo har yanzu. A dalilin rashin bin irin tsarin farko ya sa wannan dodo yake samun matsala a tsakaninsa da mutanen gari, wanda a wasu lokuta ake fatattakar shi da mabiyansa.”
Game da hanin daukar hoton dodon, Bala Ibrahim ya ce sauran dodanni ana daukar hotonsu, amma shi an hana daukar hotonsa ne saboda tsoron kada hoton ya zama abun da za a rika amfani da shi wajen barazanar mutuwa ga wadanda suka ga hoton kuma suka yarda da shi. Akwai bambanci kwarai a tsakanin irin dodon Oloolu, na da can da na yanzu domin mafi yawancin mabiyansa a yanzu za ka taras mutane ne wadanda ba su san ciwon kansu ba da ’yan banga masu tare motoci a kan hanyoyi suna tilasta karbar kudi daga hannun mutane.”