✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fiye da mutum 200 suka mutu a girgizar kasar Pakistan

Girgizar kasar da aka yi a yankin Baluchistan da ke kasar Pakistan, a kan iyakar kasar da Iran, ya haifar da asarar rayuka fiye da…

Girgizar kasar da aka yi a yankin Baluchistan da ke kasar Pakistan, a kan iyakar kasar da Iran, ya haifar da asarar rayuka fiye da 200, inda gidaujen laka suka zube, suka danne mutane. Wannan girgizar ta auku ne a ranar  Talatar da ta gabata, kafin daga bisani ta karade wasu sassan Kudancin Asiya.
Gidaje da dama sun rushe, kuma harkokin sadarwa sun tsaya cik a gundumar Awaran. karfin girgizar kasar ya samar da bullowar wani dan tsibiri a gabar tekun kasashen Larabawa.
“Tuni muka fara binne wadanda suka mutu,” a cewar Abdul Rasheed Gogazal, mataimakin Kwamishina a Awaran, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, a wata hira da suka yi da shi ta wayar tarho. Ya ce akalla mutum 373 ne suka samu raunuka.
An yi amfani da kananan jiragen sama, don kai sojoji su gudanar da ayukan ceto a yankin, a wannan yanki da aka saba yin girgizar kasa, a wata sahara da ke kan iyakar tsaunukan da ke tsakanin kasashen Iran da Afghanistan. Sashen nazarin girgizar kasa na Amurka ya bayyana cewa karfin girgizar ya kai 7.8. Can kuwa a gabar mashigin ruwa Gwadar, mazauna yankin wadanda ke cike da rudu, sun tsaya ne suna kallon ikon Allah, ganin yadda tsibiri ya bullo a sakiya ruwa.