✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fiye da mutum 300 ne za su amfana da tallafin Hukumar SEMA a Jihar Borno

Sakamakon gobarar da ta yi sanadiyyar kone wasu gidaje a wasu sansanonin ’yan gudun hijira a kananan hukumomin Gubio da Marte, Hukumar Bayar da Agajin …

Sakamakon gobarar da ta yi sanadiyyar kone wasu gidaje a wasu sansanonin ’yan gudun hijira a kananan hukumomin Gubio da Marte, Hukumar Bayar da Agajin  Gaggawa ta Hihar Borno (SEMA), da hadin gwiwar Kwamitin Shugaban Kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI), sun samar da kayayyakin taimakon agajin gaggawa don tallafa wa mutanen da abin ya shafa.

Shugaban Hukumar SEMA ta Jihar Hajiya Yabawa Kolo, ta shaida wa wakilinmu haka a garin Maiduguri a karshen makon jiya.

Hajiya Yabawa Kolo, ta ce “Akwai kananan hukumomi 4 da bala’in gobara ya auka musu musamman a sansanonin ’yan gudun hijira da suka hada da Monguno da Marte da Gubiyo da kuma Nganzai, kuma babu shakka gwamnati ta nuna bakin ciki da aukuwar wannan al’amari.”

Ta ce a baya gwamnatin jihar ta kai dauki ga kananan hukumomin Monguno da Nganzai amma a wannan lokaci sai aka hada da kananan hukumomin Gubiyo da  Marte.

Ta ce a Karamar Hukumar Gubiyo gidaje 235 ne suka kone yayin da a Karamar Hukumar Marte gidaje 95 ne suka kone, an kuma samu mutuwar mutum 3 don haka ne suka harhada kayayyakin taimakon agajin gaggawa na bukatun yau da kullum musamman kayan abinci da fiye da mutum 300 za su amfana don tallafa musu.

Ta ce gidajen da suka kone, gidaje ne na leda da kungiyoyin bayar da agaji na duniya suke samarwa. “To a kan haka ne mutanenmu suke yin girki a ciki da hakan ke sa komai zai iya faruwa,” inji ta.

Sai dai ta ce akwai bukatar a rika wayar musu da kai don gudun kada haka ya sake faruwa a nan gaba.

Shugaban Karamar Hukumar Gubiyo, Zanna Modu Gubiyo, ya tabbatar da aukuwar al’amarin inda ya ce mutum 235 ne abin ya rutsa da su a kauyen Jetara da Zowo.