✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FOMWAN na bunkasa rayuwar matan karkara – Halima

Hajiya Halima Jibril ita ce Shugabar Kungiyar Tarayya Matan Musulmi ta Kasa (FOMWAN). A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana muhimman ayyukan kungiyar da nasarori da…

Hajiya Halima Jibril ita ce Shugabar Kungiyar Tarayya Matan Musulmi ta Kasa (FOMWAN). A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana muhimman ayyukan kungiyar da nasarori da ta cimma kawo yanzu da sauran batuttuwa da suka shafi al’umma baki daya musamman mata da kananan yara.

Me ya ba ki sha’awar shiga Kungiyar Mata Musulmi (FOMWAN) har kika kai matsayin shugabarta a yau?

Da farko na samu kasancewa daya daga cikin wadanda suka fara kafa kungiyar nan a nan Najeriya, inda na kai kimanin shekara 34 ina cikinta. Ni na fara shugabancin kungiyar ta kasa bayan kafata. Na kuma rike mukamin mai magana da yawun kungiyar ta kasa. Na rike mukamai daban-daban a rassan jihohin kasar nan ciki har da na sashin ilimi na kungiyar da sauransu. Da aka kawo shawarar kafa kungiyar sai na ga ya dace in kasance a ciki ni ma in bada gudunmawata a bangaren bunkasa addinin Musulunci a kasar nan baki daya musamman a bangaren tallafa wa mata da yara da marasa galihun cikin al’umma da sauransu. Saboda haka a takaice zan ce bayan na gamsu da kudirorin kungiyar da suka hada da bunkasa Musulunci da hada kan al’ummar Musulmi musamman mata ne sai na ga ya dace in shiga in bauta wa mahallicina ta wannan bangare. Kuma a yanzu ina tabbatar maka cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu kungiyar tana cimma wadannan kyawawan kudirori a kasar nan baki daya cikin yardar Allah. Kuma a kullum ina cikin farin ciki da annasuwa a rayuwata sakamakon haka.

Wadanne nasarori kungiyar ta samu musamman a lokacin shugabancinki?

Wato ita kungiyarmu Fomwan kungiya ce da ta lura cewa al’ummar kasar nan musamman mazauna yankunan karkara suna matukar fuskantar kuncin rayuwa kuma suna bukatar ingantaccen ilimi da tallafi a kusan dukkan bangarorin rayuwarsu. Shi ya sa a yanzu muke yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin mun isar da sako da tallafi ga wadannan al’umma kai-tsaye. Wato wannan wani tsari ne na musamman da ya bambanta da ayyukan raya karkara da sauransu da muka saba yi. Misali a bangaren ayyukan raya karkara a da mukan shiga kauye ne idan muka lura ba su da ruwanm sha sai mu samar musu da shi ta shugabanninsu da sauransu ba tare da mun gudanar da cikakken bincike da ya dace ba. Amma a wannan sabon tsarin muna kokari ne mu ga mun rika yin zama na musamman da al’umma mu tattauna da su kai-tsaye don mu gano  ainihin matsalolinsu da kuma yadda suke so a magance musu matsalolin.

Ka ga ta wannan hanya duk hanyoyin magance matsalolin da suka bayyana da kansu za a iya yin haka kuma cikin sauki. A nan idan wadannan bukatu sun fi karfinmu za mu iya ba su shawarwarin da za su taimaka musu wajen samun mafita cikin sauri. Bayan wannan kungiyarmu tana aiki a bangaren kiwon lafiya da na ilimi da sauransu. A yanzu mun kafa makarantun sakandare da na rainon yara da firamare na FOMWAN a jihohin kasar nan 27. Kuma wadannan makarantu suna samar wa dimbin al’ummar kasar nan ingantaccen ilimin addini da na zamani. Kuma a kowace shekara mukan gudanar da lacca a kan muhimmancin ilimi musamman ga rayuwar ’ya mace da marasa galihu da nakasassu da sauransu kuma wannan taron lacca na shekara da ya gabata mun gudanar da shi ne a Jihar Osun inda muka tattauna a kan batuttuwan da suka shafi ilimin almajirai da na sauran kananan yara da hanyoyin tallafa musu don su samu damar farawa ko ci gaba da neman ilimi don canja rayuwarsu baki daya. Don kamar yadda binciken Hukumar UNICEF ya nuna kwanakin baya, kimanin yara miliyan 13 ne a nan Najeriya ba sa tafiya makaranta a yanzu. Ka ga wannan yana nufin akwai babbar matsala a fannin ke nan. Kuma kashi 60 cikin 100 na wadannan yara mata ne. Shi ya sa muke ganin ya kamata mu yi iya kokarinmu mu turo mata da yawa makaranta. Shi ya sa a yanzu dukkan shiyoyin kungiyarmu na jihohin kasar nan suna kamfen na a tura yaranmu mata makarantun zamani don inganta rayuwansu. Akwai kuma wani shiri na musamman da muka fara aiwatarwa a jihohin Katsina da Bauchi inda muke tuntubar iyayen yaran da suka daina tafiya makaranta sakamakon talauci da sauransu inda muke koyar da su darasi kyauta. Muna gudanar da shirin ne da hadin gwiwar wata kungiya da ake kira Northern Education Initiatibe da ke da hedikwata a jihohin Sakkwato da Kebbi. A bangaren kiwon lafiya kuma kamar yadda aka sani a kasar nan mun kirkiro tare da aiwatar da wani shiri na musamman don isar da sakonnin kiwon lafiya ta yin amfani da faifan bidiyo a manyan harsunan kasar nan wato Hausa da Ibo da Yarbanci, har ma da burokin inda muke sa wadannan faya-fayen isar da sako a gidajen rediyo da talabijin da sauransu muna fadakar da al’umma baki daya a kan batuttuwa da za su kare lafiyarsu. Kuma mukan raba wa mutane faifan bidiyon kyauta suna saurara su kalla suna kuma amfana da sakonnin da suka hada da na hanyoyin kare kai ko rigakafi daga cutar maleriya da tari da kanjamau da sauransu.

Ko kuna fuskantar matsala a yayin gudanar da harkokinku?

A gaskiya ina so in yi amfani da wannan dama in gode wa Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatotin kasar nan a dukkan matakai da kungiyoyin agaji da wadansu daga cikin masu hannu da shuni da sauransu wadanda suka san ya kamata dangane da tallafi daban-daban da  suke ba mu don inganta harkokinmu a jihohin kasar nan baki daya. Kuma a gaskiya muna bukatar ci gaba da samun wannan tallafi don kamar yadda ka sani aikin hidimar kasar nan musamman a bangaren mata da kananan yara ba karamin jan aiki ba ne.