✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fostar Lamido da Amaechi ta mamaye jihohin Yarbawa

Yanzu haka fosta-fostar Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da takwaransa na Ribas Rotimi Amaechi sun mamaye wasu daga cikin jihohin Yarbawa a wani abu…

Yanzu haka fosta-fostar Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da takwaransa na Ribas Rotimi Amaechi sun mamaye wasu daga cikin jihohin Yarbawa a wani abu da ake ganin kamar daukar mataki ne da wasu fitattun magoya bayan Jam’iyyar PDP jihoshin Kudu maso Yamma suka fara dauka don juya baya ga Shugaba Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2015.
Wadannan fosta-fosta sun fara bayyana ne a karshen makon jiyal lokacin da aka wayi gari hotunan na Gwamna Sule Lamido a matsayin dan takarar Shugaban kasa da Gwamna Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa a zaben na 2015.
Wata kungiyar Yarbawa mai suna Iwa Golden Club ce ta dauki alhakin manna wadannan fosta-fosta a bangwayen kan hanyoyi da wuraren taruwar jama’a a garuruwan Yarbawan.
A birnin Ibadan, wakilinmu ya yi kicibis da irin wadannan fosta na Gwamna Lamido da Gwamna Amaechi tare da bayanai da harsunan Yarbanci da Ingilishi kamar haka” “HAA NIGERIA A KU ORIRE O”, “Progressibe President”, “Fun Odun 2015, Edibo fun awon eniyan Onitesiwaju”, “Progressibe People, awon lole gba wa la ni Nigeria.”
Ma’ana, “’Yan Najeriya Barkanku da arziki. Ku jefa kuri’unku ga mutane masu son ci gaba a zaben shekara ta 2015. Mutane masu son ci gaba ne za su iya ceto Najeriya.”
Wakilimu ya samu tabbacin bayyanar irin wadannan hotuna a garuruwn Osogbo a Jihar Osun da Akure a Jihar Ondo.
Bayyanar wadannan fosta-fosta ta zo ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe ta kasa (INEC), ta ce, fara kamfe din zaben shekarar 2015 a yanzu ya saba wa dokokin zabe na kasa.
Kakakin Hukumar INEC, Mista Nick Dazan ne ya bayyana haka a hirarsa da sashin Hausa na Rediyon BBC, Landan a farkon mako.
daya daga cikin kusoshin Jam’iyyar PDP a Jihar Oyo Alhaji Hassan Omo Oba ya fitar da wata takardar ga ’yan jarida a Ibadan, inda a ciki ya ce, Tabbas muna goyon bayan Gwamna Lamido, ya amsa kiran jama’a na tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015.
Ya ce, “Ina wannan kira ne domin ganin ya cancanci rike wannan mukami saboda irin kyakkyawan shugabancinsa da irin rawar da ya taka a fagen siyasa tun zamanin Jamhuriya ta Biyu inda ya fito fili ya kyamaci siyasar kabilanci. Irin wannan mutum ne Najeriya take bukata.”
Ya yi misali da hangen nesan Gwamna Lamido na shirya babban taron bunkasa tattalin arziki da zuba jari da tsohonShugaban kasa Olusegun Obasanjo da Sanata Lord Paul Boateg daga Ingila suka halarta a garin Dutse.