✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

France 2019:  Super Falcons ta farfado bayan ta lallasa Korea Republic

A shekaranjiya Laraba  kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons ta yi abin kirki bayan ta lallasa takwararta ta Korea Republic da ci 2-0 a ci…

A shekaranjiya Laraba  kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons ta yi abin kirki bayan ta lallasa takwararta ta Korea Republic da ci 2-0 a ci gaba da fafafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da yanzu haka yake gudana a Faransa.

A wasan farko Norway ce ta lallasa Najeriya da ci 3-0.

Sai dai yanzu Najeriya ta farfado kuma za ta hadu a wasanta na uku ne da kasar Faransa mai masaukin baki a ranar Litinin.

Kyaftin din kungiyar Asisat Oshola ce ta jefa kwallo ta biyu a ragar Korea Republic yayin da kwallon farko ’yar Korea ce ta ci gidansu (own goal).

Idan ’yan matan suka samu nasara ko kunnen doki a wasansu na gaba, za su haye mataki na gaba.  Amma idan suka sake Faransa ta lallasa su, to sai buzunsu, don za su yi ban kwana da gasar tun ba a je ko’ina ba.

Kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu da Kamaru ne suke wakiltar Nahiyar Afirka a wannan gasa.