Aminiya

Fulani sun bukaci a fallasa mutanen da sojoji suka kama sanye da kayan soja a Kudancin Kaduna

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna Ali A. Janga

Al’ummar Fulani da  ke Kudancin Kaduna sun koka kan gum da aka yi kan wadansu mutane hudu da aka kama sanye da kayan sojoji  kuma dauke da makami a dajin Asso da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, inda suka yi kira ga hukumomi su bayyana wa duniya mutanen da suka kama kamar yadda suka saba don duniya ta san wadanda ke yawan haddasa tashin hankali a yankin.

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa ne ya bayyana haka, inda ya ce, “Bayan na samu labari daga ’yan uwanmu makiyaya na jin karar harbe-harbe a ranar na je ofishin ’yan sanda na Kafanchan na fada musu halin da ake ciki. Zuwa yamma sai na samu labarin sojoji sun yi kicibis da wadansu daga cikin mutanen sanye da kayan sojoji da bindiga kirar gida da adduna da itatuwa inda suka kama su suka kai su barikinsu da ke garin Kafanchan.”

ADVERTISEMENT

Ya ce bayan ya je barikin ya nuna musu bai kamata su ci gaba da rike su ba su mika su ga ’yan sanda domin bincike, wanda hakan ya sa washegari suka kai su hedkwatar ’yan sanda ta Kafanchan inda har yanzu ba su ji wani karin bayani a kai ba.

“In da a ce mutanen nan sun yi nasarar kai hari ko yin kisa da tuni ka ji kafafen watsa labarai na kusa da na nesa sun shiga babatu suna fadin karya da gaskiya tare da jingina wa Fulani makiyaya musamman a wannan wurin da ya yi kaurin suna wajen kai hari ana kashe mutane.

ADVERTISEMENT

Bayan kai su ofishin ’yan sanda na je da kaina inda na gansu tare da makaman da aka kama su da su, don haka ni ganau ne ba jiyau ba saboda haka adalcin da muke rokon a yi mana shi ne a fallasa sunayen wadannan mutane don duniya ta shaida farfagandar da aka dade ana yayatawa a kan Fulani makiyaya a duk wani hari da aka kai a Kudancin Kaduna ba tare da bincike ba. Wannan ita ce kafar da za mu yi amfani da ita wajen bayyana damuwarmu tare da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa su ce sun kama wadansu mutane dauke da makami sanye da kayan sojoji tare da bayyana sunayensu. Kuma muna so a bayyana wa duniya ko mutanen ’yan fashi da makami ne ko mafarauta ne ko masu garkuwa da mutane ne ko su ne masu kai hare-haren ta’addanci da aka dade ana yi a yankin tare da dora wa Fulani laifin,” inji shugaban.

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano sunayen mutanen guda hudu da aka kama kamar haka; Christian Olu da Albert Bashir da Joel Reuben da Joel James dukkansu daga garin Tanda a Masarautar Kagoma da ke Karamar Hukumar Jama’a. Hakazalika, Aminiya ta jiyo daga wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto suna ofishin ’yan sanda na Kafanchan don ci gaba da bincike, kuma sun ce sun fito ne don gabatar da wasan kwaikwayo don nuna murnarsu ga zagayowar ranar samun ’yancin kan Najeriya.