✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani sun yi bikin wankan sarauta a Randa Abeokuta

Sarakuna da shugabannin kungiyoyin Fulani da mukarrabansu a sashen Kudu maso Yamma, sun yi bikin shekara ta uku da nadin Sarkin Fulanin Randa Abeokuta, Alhaji…

Masu rawa da waka na Himma Sabon Tashi ke nan yayin da suke cashewaSarakuna da shugabannin kungiyoyin Fulani da mukarrabansu a sashen Kudu maso Yamma, sun yi bikin shekara ta uku da nadin Sarkin Fulanin Randa Abeokuta, Alhaji Kabir Muhammad Labar. An kuma kaddamar da asusun karasa aikin gina babban ofishin sarkin da ke kasuwar shanu ta Randa din.
 Cikin jawabinsa, a matsayin babban bako mai kaddamarwa, Gwamna Ibikunle Amosun na Jihar Ogun, wanda Sakataren gwamnati, Barista Taiwo Ade-Oluwa ya wakilta, ya nemi Fulanin da ke zaune a jihar su saki jiki, su mike kafa domin gwamnati tana tare da su a kowane lokaci. Haka nan ya bukaci shugabanni su mayar da hankali wajen wayar da kan jama’arsu game da muhimmancin zaman lafiya da kiyaye dokokin kasa.
 Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Mai Yasin, uban taro da shugaban kungiyar sarakuna da shugabannin Fulani na kasa, Sarkin Fulanin Jihar Legas, Alhaji Muhammad Abubakar Bambado, sun yi jawabai da suka fi mayar da hankali a game matakan shawo kan matsalar rikicin makiyaya da manoma, wadda suka nuna farin cikin ganin an fara samun nasara kanta. Batun da ake ganin ya rage shi ne na samo hanyar kyautata zamantakewar Fulanin da kuma jama’ar garin da suke zaune.
 Mai masaukin baki, Sarkin Fulanin Randa, Alhaji Kabir Muhammad Labar ya jinjina wa Gwamna Ibikunle Amosun game da kafa kwamitocin hadin guiwa da sakataren gwamnati ya shugabance su, wadanda suka yi maganin matsalar rikicin tsakanin Fulani da manoma da ke Ketu cikin karamar Hukumar Yewa ta Arewa. “Muna kuma jinjina wa wakilai 7 na majalisar dokokin jihar ta Ogun kan ziyartar dukkan wuraren da rikicin Fulani da manoma ya shafa da lalubo hanyar magance rikicin a nan gaba. Kuma zan yi iya kokarina wajen ganin kyautatuwar zamantakewar Fulani da jama’ar gari baki daya.” Inji shi.
 Cikin wadanda suka halarci bikin har da Alhaji Zakariya’u Umar, wanda ya wakilci Daraktan tsaro na Jihar Ogun da wakilin kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Mista Somoye Adedayo da Onijaye na Ijaye, Oba Adeyemi Otunba da Oomala na Imala, Oba Apostle Moses. Shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihar ta Ogun, Alhaji Umar Muhammed da sakataren majalisar, Alhaji Inuwa Garba Sarki, su suka jagoranci sarakunan Hausawa na garuruwa daban-daban zuwa wajen bikin.
 Kodayake wakilin gwamna bai furta gudunmawa ba, jama’a da dama, musamman Fulani sun bayar da gudunmawar kudi da dabbobi da za a yi amfani das u wajen karasa aikin ginin babban ofishin Sarkin Fulanin.
 Wata kungiyar raye-raye da wake-wake mai suna Himma Sabon Tashi da aka gayyato daga kasar Nijar ta nuna wasannin al’ada ga mahalarta bikin. Sannan samarin Fulani da ’yan matansu sun yi kwalliyarsu ta kayatarwa.